Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Roma ta kori Daniele De Rossi daga matsayin mai horas wa, bayan da ƙungiyar ta gaza taɓuka kataɓus a wasannin farko na gasar Serie A da ya jagoranceta, lamarin da ya sakata zama a mataki na 16.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a Laraban nan, ta sanar da sallamar tsohon ɗan wasan tsakiyar tawagar Italiya, watanni 8 bayan da ya maye gurbin Jose Mourinho da aka kora a watan Janairu.
De Rossi wanda ke cikin tawagar Italiya da ta lashe kofin duniya na shekarar 2006, Roma ta salleme shi ne duk da cewa yana da yarjejeniya da ita har zuwa watan Yunin shekarar 2027.
Wasanni huɗu ne kaɗai De Rossi ya jagoranci Roma a gasar Serie A ta bana, kuma wasan ƙarshe da ya jagoranci ƙungiyar shi ne karawar da suka yi da Genoa a ranar Lahadi inda aka tashi 1-1, wasan da a farko aka saran zai kasance na farko da ya samu nasara a kakar wasan bana ta gasar Serie A.
Kafofin yaɗa labaran Italiya sun fara bayyana cewar akwai yiwuwar Iɓan Juric wanda ya jagoranci ƙungiyar Torino a baya-bayan, da kuma Massimiliano Allegri a matsayin waɗanda za su maye gurbin De Rossi.
