Lamine Yamal ya zura ƙwallaye biyu cikin ƙasa da minti 10 don jagorantar Barcelona zuwa ga nasara ta biyar a jere a farkon kakar gasar La Liga ta Sifaniya.
ƙwallaye biyu na matashin zan wasa da kuma ƙwallayen rabin lokaci biyu daga Dani Olmo da Pedri su suka bai wa Barcelona nasara da ci 4-1 a kan abokiyar hamayyarta ta Catalonia, Girona.
Barcelona tana da tazarar maki huɗu a saman tebur fiye da Real Madrid, Atletico Madrid da ɓillarreal.
Yamal ya fara zura ƙwallon farko bayan ya kwace ƙwallo daga hannun ɗan baya sannan ya cilla ƙwallon cikin raga a minti na 30.
Ya sake zura ƙwallo a minti na 37 bayan ya ɗauki wata ƙwallo ta tsantar dami a kala.
Atletico ta doke ɓalencia mai riƙe da matsayi na ƙarshe da ci 3-0 tare da ƙwallaye daga Antoine Griezmann da sabbin ‘yan wasa Julian Alɓarez da Conor Gallagher.
