Nijeriya ta kammala wasannin gasar Paralympics na wannan shekarar inda ta kammala a mataki na 40 bayan ta lashe lambar yabo guda bakwai ciki kuwa akwai gwal guda biyu da tagulla guda uku da kuma azurfa guda biyu da aka samu a gasar.
‘Yan wasa irin su Onyinyechi Mark da Folashade Oluwafemiayo da Bose Omolayo da Flora Ugwunwa da Esther Nworgu da sau Ogunkunle su ne suka lashewa Nijeriya waɗannan kyaututtukan a wannan shekarar da aka kammala.
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kammala wasannin gasar nakasassu da ya haɗa ’yan wasa daga ƙasashe daban-daban na Duniya kamar yadda aka kammala na masu lafiya a watan da ya gabata a ƙasar ta Faransa.
Sai dai daman tun farko hukumomin Birnin na Paris sun yi alƙawarin gudanar da gasar da za a daɗe ana tuna ta yayin da suke shirin karɓar baƙuncin gasar Olympics ta nakasassu ta wannan shekara ta 2024.
Bayan da aka yi gasar wasannin Tokyo a 2021 ba tare da ‘yan kallo ba saboda Annobar Korona, sannan ita kuma gasar Rio ta 2016 ta gamu da matsalollin kuɗi, Birnin Paris ya kasance cikin matsin lamba kan ya gudanar da gasar da za ta kasance daidai da wadda aka yi a Birnin Landan a 2012 ko ma gasar ta Paris ta zarta ta.
Bikin buɗe gasar da za a ranar Larabar da ta gabata da karfe 7:00 na yamma agogon
Nijeriya zai kasance ne a ‘Place de la Concorde’, inda za a bayar da kyaututtuka na lambobin Zinare 549 ga ‘yan wasan da suka yi bajinta a washegari.
Sannan an kammala gasar inda aka yi bikin rufewa a filin wasa na Stade de France ranr Lahadi 8 ga watan Satumba 2024, sannan an sayar da tikiti kusan miliyn biyu na shiga gasar zuwa yanzu, inda kuma har yanzu akwai 500,000 da ba a saya ba. Bayan irin nasarar da aka samu ta gasar Olympics da aka kammala a Paris hukumomin birnin sun ce wannan somin-tabi ne.
Gasar ta Paris ta samu ‘yan wasa mata da tawagogin ‘yan wasa da ba a taba samu ba a wata gasa ta nakasassu ta Olympics, sannan kuma za a nuna a tashoshin talabijin a yankuna da dama masu yawan da ba a taɓa yi ba a baya.
Kuma Faransa ba ta taba karɓar baƙuncin wasannin nakasassu na bazara ba, koda yake ta karbi baƙuncin wasannin lokacin hunturu na 1992 da aka yi a Albertbille.
