Lauyoyin ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe, sun ce sun ƙi amincewa da buƙatar Hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar LFP, na shiga tsakanin ɗan wasan da tsohuwar ƙungiyarsa ta PSG, kan taƙaddamar rashin biyansa wasu haƙƙoƙinsa.
Mbappe dai ya yi ikirarin yana bin ƙungiyar kuɗin da suka kai Euro miliyan 55, sai dai ƙungiyar ta PSG ta ce ɗan wasan ya yafe mata waɗannan kuɗaɗe a watan Agustan shekarar bara.
A ranar Laraba ne dai lauyoyin ɓangarorin biyu suka gana, bayan da Mbappe ya gabatar da ƙararsa a gaban kwamitin kula al’amuran shari’a na hukumar ta LFP, lamarin da ya sa taso yin sulhu a tsakanin ɓangarorin biyu.
Tuni dai ɓangaren ƙungiyar PSG ya ce ya goyi bayan yin sulhu a tsakaninsu, inda ta ce ta daɗe tana neman irin wannan dama.
A ƙarshen kakar shekarar da ta gabata ne dai Kylian Mbappe ya raba gari da tsohuwar ƙungiyarsa PSG, inda ya koma ƙungiyar Real Madrid don ci gaba da wasansa a can.
