Tawagar ‘yan sanda da sojoji sun yi wa gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki rakiya daga babban ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ke birnin Benin.
Mataimakin Sufeto Janar (DIG), Frank Mba, ya fitar da Obaseki daga harabar da karfe 4:10 na safiyar Lahadi.
Gwamnan ya isa ofishin hukumar zaɓen ne da misalin karfe 2 na safe, inda yake nuna rashin amincewarsa da rashin bayyana sakamakon zaɓen ƙaramar hukumarsa ta Oredo.
Sai dai an ce jami’ai sun sanar da shi cewa bai kamata ya kasance a harabar ba.
Sai dai an ce gwamnan ya dage da zama, lamarin da ya sa tawagar ‘yan sanda da sojoji ƙarƙashin jagorancin DIG Mba suka shiga harabar hukumar ta INEC, suka yi wa Obaseki rakiya.
