Waƙa: Ƙarshen Tika Tiki

Spread the love

Tare da MURTALA UBA MUHAMMED 

Mai ɗauka ran mutane,

Mai shiga daji ya zaune,

Kui faɗi masa don ya gane,

Tasa ma na nan tahowa. 

Mai fashi da kisa da gangan,

Ran da za ka mace a rannan,

Babu Allah kai jiƙan nan,

Sai la’anta ke biyowa.

Wani bai ji ba bai sani ba,

Wani bai taɓa ko ashar ba,

Wani bai taɓa zambata ba,

Wani bai cutar da kowa. 

Ba ka bar shi ba kai kisan sa,

Ka raba shi da dukiyarsa,

Ka raba shi da lafiyarsa,

Taka sannu tana tahowa. 

Kai da ke cutar mutane,

Kai fitsari kan faƙo ne,

Zai zubo maka kan tufa ne,

Kai fa kanka kake kashewa. 

Duk sanda ka ɗau waninka,

Tamkar ka ɗauki ranka,

Domin fa suna wuyanka,

Lahira da akwai tilawa. 

Shi fa mai ɗaukan mutane,

Zai mace tsaye ko a zaune,

Ko a kar shi kamar kare ne,

Kai kare yai mas ɗarawa.

Cutar da ya yiwa bayi,

Rabbana na nan Buwahi,

Zai yi sakayya Ilahi,

In ya so ba ya gusawa.

By ukarofi