Alaƙata da masu karatun littattafaina alaƙa ce mai ban sha’awa da burgewa
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Komar shafin Adabi a wannan mako ta yiwo babban kamu ne daga tekun marubutan adabi, inda wakilin Manhaja Blueprint, Abab Abubakar Yakubu, ya samu nasarar tattaunawa da jajirtacciyar marubuciya, ‘yar kasuwa, malama, kuma mawallafiyar waƙoƙin yabon manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW), Malama Fauziyya Sani Jibrin, marubuciyar littafin ɗalibai da wasu da dama, wacce ƙwarewarta wajen rubuta gajerun labarai ya sa ta samun nasarori masu yawa, a gasanni daban-daban na marubuta. Tana daga cikin marubutan onlayin waɗanda baiwarsu da natsuwar su wajen kiyaye ƙa’idojin rubutu ya sa cikin lokaci ƙanƙani tauraruwarta ta haskaka. A zantawarta da wakilinmu Fauziyya ta bayyana masa tasirin mahaifiyarta a rubuce-rubucen da take yi.
MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.
FAUZIYYA: Sunana Fauziyya Sani Jibril. Wasu suna kira na da Aunty Baby. Asali suna ne da mahaifiyata take kira na da shi kasancewa ta ɗiyar fari, don haka saboda alkunya, ba ta faɗar sunana na haƙiƙa sai dai ta kira ni da Baby. Daga haka ne sunan ya samo asali.
Na taɓa koyarwa a makarantun Islamiyya, na koyar a makarantar Nurul Islam, da kuma Mahmud Islamiyya, sannan kuma na taɓa buɗe makaranta a gidan mijina, don koyar da yara ƙarin hasken ilimi, wato Lesson School, a ɓangaren ilimin addini da na boko, musamman koyon rubutu da karatun Hausa. Amma ban daɗe sosai ina gudanar da makarantar ba na daina, saboda wasu dalilai da dama.
A yanzu dai ni ‘yar kasuwa ce da ke sana’ar sayar da kaya iri-iri, wato collections, kamar su kayan kicin, atamfofi, shadddodi, leshuna, yaduna, hijabai, huluna, mayafai, takalma, jakunkuna, turaruka, yari da sarƙa. Da kayan ƙwalama irinsu snacks, juice, candy’s, har zuwa kan grain mills, wato garin kayan abinci, kamar su garin ɗanwake, garin dawa, garin masara, na kunu, da na alkama. Bugu da ƙari kuma ga rubutu da nake yi, don shi ma babbar sana’a ce.
Ina da aure, kuma Allah Ya albarkaci aurenmu da samun ‘ya’ya shida, maza biyu mata huɗu, yanzu haka ina zaune a unguwar Sani Mainagge ‘A’ Islamiyya Avenue.
Ki ba mu tarihin rayuwarki.
Ni ‘yar asalin Jihar Kano ce, daga ƙaramar Hukumar Gwale, unguwar Sudawa. An haife ni a ranar 23 ga watan Nuwamba shekara ta 1989. Na yi makarantar Islamiyya inda na sauke Alƙur’ani Mai Girma, da wasu littattafan addini a makarantar Gwadabe Maitasa Islamiyya. A makarantar Abdullahi Mai Masallaci na fara koyon haddar Alƙur’ani amma ban kammala. Na yi karatun firamare a ɗandago Special Primary School. Na kuma shiga karatun sakandire a Makarantar ‘Ƴammata ta Sani Mainagge Secondary School. Na rubuta jarabawar fita daga sakandire a Makarantar ‘Yammata ta GGASS ƙofar Na’isa. Sannan na karatun koyon aikin malanta na N.C.E a Kwalejin Ilimi ta Aminu Kano, inda na karanci Hausa da ilimin addinin Musulunci. Zuwa yanzu dai matakin karatuna na NCE ne, amma akwai yiwuwar cigaba da karatun a kusa, idan Allah Ya nufa.
Ki bamu labarin yadda rayuwa ta kasance miki yayin tasowarki, wacce irin gwagwarmaya aka fuskanta?
To, ni dai gaskiya babu abin da zan ce da Allah sai godiya, Alhamdulillah. Domin na taso cikin gata, na kuma samu kulawa da hidimtawa, gami da nuna ƙauna yadda ya kamata daga wajen iyayena. Mahaifiyarmu ta sha fama da gwagwarmaya wajen ba mu kyakkyawar tarbiyya, mahaifinmu ya kasance jajirtaccen mutum ne, wanda ya tsaya tsayin daka wajen ba mu ingantaccen ilimi, ga shi kuma Alhamdulillahi, har yanzu muna cin gajiyar ilimin. Ba don ilimin da na samu ba, da ban zama Marubuciya ba, domin sai da ilimi za a iya rubutun har a san abin da ya kamata a rubuta, don haka jahili ba zai taɓa zama Marubuci ba.
Wanne ƙalubale kika fuskanta da ya koya miki wani muhimmin darasi a rayuwarki?
Na sha fuskantar ƙalubale iri-iri, a mabambantan lokuta, domin ita rayuwa dama ba a raba ta da ƙalubale, amma Alhamdulillahi. Duk ƙalubalen da na fuskanta a rayuwa na kan bi shi da addu’a, don haka cikin sauƙi nake samun mafita. Zan iya cewa akasari ƙalubalen da na samu wanda ba zan manta da shi ba, akan batun neman ilimi ne. Lokacin ina ƙarama ina yawan makara wajen zuwa makarantar Islamiyya, kasancewar sai an dawo daga makarantar boko an ci abinci, an yi wanka da yin sallah, sannan a tafi Islamiyya. Hakan ya sa muke yawan makara ni da ƙanwata, mu kuma ga mu da tsoron duka, don haka kusan kullum da kuka muke tafiya, saboda tsoron dukan makarar da za mu riska. Sai da muka ƙara wayo sannan muke tafiya da abincinmu, ko idan an fita sallar La’asar mu koma gida mu ci. Da haka ne muka samu sauƙin dukan makara.
Wanne abu ne za ki iya cewa, ya taimaka wajen mayar da ke irin macen da yanzu kika zama.
Abin da ya taimaka na kai matakin da nake a yanzu, shi ma dai ba zai wuce irin kulawar da iyaye suka ba ni ba, don ilimi ko yaya yake yakan sa a taka wani matsayi na ɗaukaka a rayuwa. Sannan kuma haƙuri da juriyar gwagwarmayar rayuwa, suna jawo cigaban rayuwa. Domin duk abin da ya tunkaro mutum na jarrabawar rayuwa, idan aka sa haƙuri kuma aka jure, wannan jarrabawa za ta zama tarihi. Kuma za a samu nasara a rayuwa, tun da Allah Ya ce Yana tare da masu haƙuri, kuma dukkan tsanani yana tare da sauƙi, babu wani yanayi da yake dawwama sai ikon Allah.
Mene ne ya ja hankalinki kan rubutun adabi?
Abin da ya ja hankalina kan rubutun adabi shi ne, yadda marubuta suke samun damar isar da saƙo ga al’umma cikin sauƙi ta hanyar rubutunsu, kuma saƙon ya yi tasiri fiye da yadda yake yi, idan an bi ta wata hanyar wadda ba ta rubutun ba. Wannan dalilin shi ne ya busa wa burina na zama marubuciya ruhi.
Yadda aka yi na zama marubuciya da kuma hanyoyin da na bi kafin na fara rubutu kuwa su ne. Da farko dai rubutu burin mahaifiyata ne, Allah Ya cika mata wannan buri nata a kaina, ma’abociyar karatun littattafai ce don haka ita ma ta so zama marubuciya Allah bai nufa ba, kuma tun muna ƙanana ta kan karanta mana littattafan da suka yi daidai da shekarunmu, ni ma na kan je na ba wa ƙawayena labarin da ta karanta mana, sai yadda suke jin daɗin labarin ya dinga burge ni, da haka son yin rubutu ya ɗarsu a zuciyata, burin yin rubutun ya ƙaru ne dalilin karantar Hausa da na yi. Bayan na kammala karatuna na N.C.E sai na nemi yardar mijina da ta iyayena a kan ina son fara rubutu, sai suka amince tare da saka mini albarka.
Yaushe kika fara tunanin fara rubuta labarin kanki, kuma ko za ki iya tuna yaya labarin yake?
Yadda aka yi na fara rubutu shi ne, bayan iyayena da maigidana sun amince na fara rubutu tare da saka mini albarka, sai na tashi ƙafa da ƙafa na je gidan ƙawata abokiyar karatuna, wacce yanzu Allah ya haskaka tauraronta ta zama shahararriyar Marubuciya, wato Hassana Labaran ɗanlarabawa. Na nemi shawararta akan burin da nake da shi na son fara rubutu, sai ta nuna min jin daɗinta tare da bani ingantattun shawarwari. Daga nan kuma sai ta ba ni lambar Malam Abubakar Sadik, ta ce na neme shi zai saka ni a ƙungiya.
Bayan shiga ta ƙungiyar, sai na fahimci wasu abubuwa dangane da rubutu, don haka sai na fara rubuta labarina mai suna ‘Zuciya ɗaya’, amma ba shi ne labarin da na fara fitarwa ba, saboda rasa shi da na yi a lokacin sanadiyyar lalacewar waya, hakan ya sa kawai na fitar da wani labarin mai suna ‘Zulaihat’. Da farko gajeren labari na yi niyyar rubutawa, amma yadda na ga ya samu karɓuwa sosai, da kiran da masu karanta labarin suka dinga yi, cewar don Allah in cigaba sun ji daɗin labarin ya sa na faɗaɗa shi zuwa dogon labari. Labarin ‘Zulaihat’ labari ne na wata matashiya da ta dinga haɗuwa da ƙalubalen rayuwa iri-iri, tun tana zanin goyo har ta girma, da irin gallazawar da mariƙiyarta ta dinga yi mata. Jigon labarin shi ne, illolin wulaƙanta ɗan’adam, da irin nasarori da ɗaukakar da wanda aka ƙasƙanta yake samu, ta yiwu ma ya zama shugaban mutanen da suka raina shi a baya, ko wani mai faɗa a ji.
Kawo yanzu kin rubuta littattafai guda nawa? Kawo sunayensu da bitar uku daga ciki.
Kawo yanzu dai zan iya cewa, na rubuta labarai guda 10, amma mafi yawancinsu gajerun labarai ne. Labaran sun haɗa da ‘Zulaihat’, ‘Maula’, ‘ƙwange’, ‘Hasken Mafita’, ‘ɗalibai’, ‘Tuwon Tulu’, ‘Tubalin Toka’, ‘Ba A Yin Ruɗe’, ‘Babu Rashi Ga Allah’, sai kuma ‘Zuciya ɗaya’.
Fitattu daga cikin littattafan da na rubuta, kamar yadda na faɗa a baya akwai labarin ‘ɗalibai’, wanda labari ne da ya zo da sabon salon da ba a faye zuwa da shi ba. Labarin ya taɓo rayuwar ɗalibai, ɓangaren malamai da kuma iyaye, har ma da gwamnati, dangane da yadda kowanne ɓangare yake da damar taka muhimmiyar rawa, wajen kawo cigaba a ilimin yara manyan gobe, domin samun nagartaccen ilimi don gina ingantacciyar al’umma. Labarin ɗalibai ya nuna muhimmancin bin ƙa’idojin koyarwa, da yadda haɗa karatu da nishaɗi yake da matuƙar tasiri wajen fahimtar karatu. Bugu da ƙari labarin ɗalibai yana ɗauke da waƙoƙi masu saka yara da manya nishaɗi, da kuma abubuwa daban-daban na ilimin zamantakewa.
Shi kuma labarin Zulaihat, labarin ne na wata matashiya da ta dinga haɗuwa da ƙalubalen rayuwa iri-iri, tun tana zanin goyo har zuwa girmanta, da irin gallazawar da mariƙiyarta ta dinga yi mata. Jigon labarin shi ne, illolin wulaƙanta ɗan’adam. Labarin ya taɓo irin nasarori da ɗaukakar da wanda aka raina yake samu. Ta iya yiwuwa ma watan wata rana ya zama shugaban mutanen da suka raina shi ko suka wulaƙanta shi, ko ma ya zame musu wani ginshiƙi a rayuwa ko wani mai faɗa a ji.
Sannan akwai labarin ‘Zuciya ɗaya’, wanda shi kuma labari ne da aka yi ɓarin sirruka iri-iri a cikinsa, na zamantakewar aure, waɗanda suke sa ma’aurata su kama zuciyoyin junansu, ta hanyar kanainaya, tarairaya da kuma nuna kulawa, da wasu sababbin hanyoyi na musamman. Zuciya ɗaya labarin wasu iyalai ne, da suka gina rayuwarsu ƙarƙashin lema guda ta aminci da yarda, shaƙuwar da take tsakaninsu ta sa jama’a suke yi musu kallon tsintsiya maɗauri ɗaya. Sai dai kuma akwai wani cukurkuɗaɗɗen al’amari, wanda bibiyar labarin har ƙarshe ne kaɗai zai sa masu karatu su fahimci cewar, da zuciya ɗaya suke zaune da junansu ko kuwa dai akwai lulluɓin Kura da fatar Akuya?
Wanne littafin ne ya fara ɗaga sunanki a tsakanin marubuta?
Labarin da ya fara ɗaga sunana a duniyar marubuta shi ne labarina mai suna ‘ɗalibai’. Labarin ya burge Manazarta da Makaranta, na samu yabawa ƙwarai da gaske akan labarin. Na karanta labarin a lokacin da aka yi hira da ni a gidan rediyon Dala FM, a shirin Duniyar Marubuta, wanda Malam Jibrin Adamu Rano yake gabatarwa a duk ranar Talata. Daga nan kuma sai na dinga samun kira da roƙo daga wajen makaranta cewar shi ma suna so don Allah na faɗaɗa musu shi ya zama dogon labari, har akwai wata baiwar Allah mai suna Maryam B. Khalil, (Maman Nasrin) da ke garin Kaduna, wacce bayan ta saurari hirar da aka yi da ni, sai ta nemi lambata ta kira ni. Ta yaba mini sosai, sannan ta yi mini alkhairai da dama. Sannan ita ma kuma ta roƙe ni kan tana so na faɗaɗa labarin, kasancewar ita ɗin malamar makaranta ce. Wannan labarin mai suna ɗalibai ya sa ta ƙara fahimtar abubuwa da dama dangane da koyarwa, duk da gajeran labari ne, ina kuma ga an ƙara faɗaɗa labarin, da kuma fito da wasu muhimman abubuwan da za su ƙara wayar da kan Malamai? Dalilan kenan da suka sa na fara tunanin faɗaɗa labarin daga gajere zuwa dogo, wanda a yanzu ina nan a kan rubutunsa, kuma zan fara fitar da shi a kurkusa da yardar Allah.
Yaya alaƙarki da masu karatun littattafanki, ta yaya kike mu’amala da su?
Alaƙata da masu karatun littattafaina alaƙa ce mai ban sha’awa da burgewa, domin akwai nuna ƙauna, mutuntawa da kuma girmamawa a tsakaninmu. Muna yin zumuci ni da masu karanta labaraina, wasu sun sha kawo mini ziyara har gida, amma mafi yawancin su sun fi kira na a waya mu gaisa, ko mu yi hira ta soshiyal midiya. Sannan sun sha yi mini kyaututtuka iri-iri, musamman kyautar data da kuma katin waya, ganin cewar ta onlayin ne nake tura musu labaran da suke karantawa. A taƙaice dai akwai kyakkyawar alaƙa tsakanina da makaranta litattafaina.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

