Gwamnatin Tinubu ta fi kowacce gwamnati a Nijeriya sauƙin sha’ani ga masu zuba hannun jari – Shettima

Spread the love

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jaddada jajircewar Gwamnatin Tarayya wajen samar da yanayin da zai taimaki masu zuba jari.

Ya bayyana hakan ne a taron kasuwanci na manyan shuwagabanni na Amurka da Nijeriya.

Shekaran farko da aka cire tallafin man fetur wanda ke zama kamar nauyi a wuyan Nijeriya, Shugaban Ƙasa Tinubu ya ɗauki matakin farko na cire tallafin man fetur da haɗa kasuwannin musayar kudi da dama.

Shettima ya bayyana haka a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai Stanley Nkwocha, ya fitar a ranar Litinin.

“Na roƙe ku, ku bai wa Nijeriya wata dama domin gwamnatin yanzu ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ita ce mafi taimako ga masu zuba jari a tarihin Najeriya,” in ji Shettima.

By ukarofi