Ka rantse da Ƙur’ani ba ka da hannu a ayyukan ta’addanci – Matawalle ga gwamnan Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya yi watsi da zargin da Gwamnan jihar, Dauda Lawal ya yi akan sa na cewa ya na da hannu acikin taimaka wa ta’addanci.

Matawalle, wanda shi ne ƙaramin ministan tsaro a Nijeriya, ya ƙalubalanci ƴan siyasa ciki har da Gwamna Dauda kan cewa su rantse da Ƙur’ani ba su da hannu acikin ayyukan ta’addanci da ya addabi jihar.

Ya ce, “Ni kaɗai ne gwamnan da ya rantse da Al-Ƙur’ani mai tsarki cewa ba ni da hannu a ayyukan ta’addanci.”

“Na ƙalubalanci duk ƴan siyasar, har da Janar Ali Gusau da Dauda Lawal su ma su yi irin hakan. Babu ɗaya daga cikin su da ya rantse. Idan kuma ba su yi rantsuwar ba, hakan ya nuna su na da hannu acikinsa”, inji Matawalle, kamar yadda ya faɗa a ranar Talata yayin hira da gidan talabijin na ‘channels’.

A kwanakin baya ne, Dauda Lawal ya yi kira ga Matawalle da ya sauƙa daga muƙaminsa don wanke kansa, ya na mai cewa tsohon gwamnan ya bai wa ƴan ta’adda mafaka a gidan gwamnatin jihar kuma a na biyan ƴan ta’adda kuɗin fansa ta hannun gwamnatin jihar.

Saidai, Matawalle ya kare hukuncinsa da ya zaɓa na tattaunawa da ƴan bindiga wanda da dama daga cikin gwamnnoni sun goyi bayan hakan inda a sakamakon haka, aka ceto mutane da aka yi garkuwa da su da dawo da wasu makamai a Zamfara.

Matawalle ya ƙara da cewa, baki ɗaya waɗanda ke zargin sa, su na da hannu a cikin ayyukan da su ke zargin nasa a akai.

Har’ilayau, ya musa zargin sauya akalar kuɗaɗen jihar inda ya ce baki ɗaya hakan ƙage ne daga Gwamnan jihar, Dauda Lawal.

Gwamna Lawal ya zargi tsohon gwamnan da sace sama da biliyan 70 daga asusun gwamnatin jihar.

By Babaji