
Kwamitin karɓar Ƙorafe-ƙorafe kan Kafafafen Yaɗa Labarai na Kasa (NMCC), ya fitar da rahotonsa kan taƙaddamar zargin goyon bayan auren jinsi a yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta sanya wa hannu ta Samoa.
Kwamitin, wanda gogaggun ƴan jarida da lauyoyi ke yi wa shugabanci, ya ce kamfanin jaridar ‘Daily Trust’ ya tafka kuskure a wancan labarin akan yarjejeniyar ta Samoa.
Binciken ya biyo bayan ƙorafin da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a ta Tarayya ta yi akan Daily Trust.
Hukumar, a cikin rahotonta mai shafuka 19, ta ce bayan ta binciki ƙorafin gwamnati da kuma martanin da jaridar tayi, ta gano labarin da jaridar ta wallafa kan yarjejeniyar Samoa a matsayin kuskure, tare da umartar jaridar ta nemi afuwar Gwamnatin Tarayya bisa abin da rahoton nasu ya jawo mata.
