Daga MAHDI M. MUHAMMAD
A wani gagarumin ci gaba da ta ke samu a fagen yaƙi da ta’addanci, Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da kawar da manyan jagorori da kwamandojin ‘yan ta’adda 65 a rubu’i na uku na shekarar 2024.
Wannan nasarar ta nuna wani gagarumin ci gaba a yaƙin da ake yi da ta’addanci a ƙasar.
Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai a Abuja.
A cewar Manjo Janar Edward Buba, dabarun da sojojin ke bi sun wargaza cibiyoyin ‘yan ta’adda yadda ya kamata tare da daƙile ayyukansu a faɗin ƙasar.
Ya bayyana fitattun jiga-jigan ’yan ta’addan aka kashe sun haɗa da Munzir Arika, Sani Dilla, Ameer Modu, da Matawal Bitrus, da sauransu.
Manjo Janar Buba ya zayyana wasu muhimman abubuwa na ƙoƙarin da sojoji suka yi na yaƙi da ta’addanci a cikin wannan lokaci da suka haɗa da kashe ‘yan ta’adda 1,937, kame mutane 2,782 da ake zargi da ta’addanci da sauran miyagun laifuka, da ceto mutane 1,854 da aka yi garkuwa da su, da ƙwato makamai 1,304 da alburusai 43,347 da kuma hana satar mai da ta kai sama da Naira biliyan 13.
“Dakarun Operation HADIN KAI sun gudanar da samame a cikin dajin Sambisa da Tumbun na yankin tafkin Chadi. Ayyukan sun fallasa kwamandojin ‘yan ta’adda da sansanonin shugabannin su.”
“A cikin kwata na uku na shekarar, sojojin Operation HADIN KAI sun kashe ‘yan ta’adda 792, sun kama mutane 606 da ake zargi da kuma kuɓutar da mutane 476 da aka yi garkuwa da su. Bugu da ƙari, sojoji sun rubuta jimillar ‘yan ta’addan Boko Haram da iyalansu 7,283 da suka miƙa wuya,” inji shi.
A cewarsa, yawan ɗanyen man da aasar ke haƙowa a kowace rana shi ma ya kai matsayin da ba a taɓa ganin irinsa ba, inda ake sa ran za a yi amfani da shi a kullum.
