Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja
A wata ganawa ta musamman da ya samu yi a ƙasar Amurka, Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashin Shettima ya samo wa ƙasar tallafin zunzurutun kuɗi Dala 600,000 daga gidauniyar Bill da Melinda Gates ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa.
Wannan wani yunƙurin gaggauta ne na samar da sauƙi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Nijeriya da kuma bunƙasa fannonin lafiya da noma, inda Gwamnatin Nijeriya ta samo tallafin na Dala 600,000 da wasu ayyukan cigaba daga gidauniyar Bill da Melinda Gates.
Gidauniyar ta yi alƙawarin bayar da Dala 600,000 a matsayin tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Borno da wasu shirye-shirye a fannin kula da lafiya tare da ƙarin Dala Miliyan Biyar daga makarantar horar da harkokin kasuwanci ta Legas da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa, don bunƙasa tattalin arziki a fannin noman rogo.
An sanar da bayar da tallafin ne a lokacin da Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya gana da ta Gidauniyar Bill da Melinda Gates ƙarƙashin jagorancin shugaban shirin gidauniyar na duniya tare da Dakta Christopher Elias, a wani ɓangare na taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York.
Mataimakin Shugaban Nijeriya, Sanata Kashim Shettima, ya jaddada himmatuwar Gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Tinubu na sanya fannin lafiya da samar da abinci mai gina jiki da bunƙasa fannin noma a matsayin sahun farko a abinda ƙasar ta sanya gaba.
“Mun himmatu matuƙa wajen magance ƙalubalen da ƙasarmu ke fuskanta, mussaman batun rashin abinci mai gina jiki,” inji Mataimakin Shugaban ƙasa Shettima. Ya ƙara da bayani kan sadaukarwar Gwamnatin Nijeriya na samar da nagartaccen shugabanci da zai magance waɗannan ƙalubalen, inda ya bayyana cewa akwai shirin gaggawa da ake na samo wuraren samar da masara a ƙarƙashin shirin ‘Telemaze’.
Da yake alƙawari kan ɗaukar matakin gaggawa game da damar shigo da iri mai kyau, Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce, “Mun lura da muhimmancin da samar da abinci da bunƙasa fannin noma na zamani yake da shi. Batun noman rogo na zamani na riƙe da ci gaban tattalin arzikinmu.
“Muna ƙoƙarin mayar da hankali kan dukkan al’amuran gwamnati zuwa tsarin fashar zamani da musayar bayanai, wanda muke da yaƙini zai kawo sauyi ga ayyukan gwamnati”, sai ya yi ƙarin bayani game da ƙoƙarin gwamnati na mayar da hankali ga ci gaban fasahar zamani.
Haka zalika, Mataimakin Shugaban ƙasa Shettima ya kuma bayyana fatan cewa “da gogewar ministocin Nijeriya” da kuma ci gaba da tallafi da ake samu daga abokan hulɗa kamar Gidauniyar Gates, “ƙasar na da ƙwarin gwiwa na ƙoƙarinta wajen kawo sauyi mai ma’ana da inganta rayuwar dukkan ‘yan Nijeriya.”
A nasa ɓangaren, Shugaban Bunƙasa Ayyukan Gidauniyar Na Duniya, Dakta Christopher Elias, ya ce, gidauniyar ta yi matuƙar damuwa kan illar da ambaliyar ruwa ta yi a Jihar Borno da kuma ƙoƙarin gidauniyar na tallafa wa Nijeriya a lokacin da ake fama da ƙalubale tare da tallafa wa fannin lafiya, musamman a yaƙi da cutar shan inna.
“Mun gamsu da ƙoƙarin kwamitin kar ta kwana na ƙasa wajen kawar da cutar shan inna zuwa ƙarshen shekara”, inji Dakta Elias.
Shi ma, Shugaban Sashin Ci Gaba Da Bunƙasa Na Gidauniyar Bill da Melinda, Rodger Voorhies, ya bayyana tsare-tsare na bunƙasa samar da masara da kuma ƙarfafa fannin shirin bunkasa samar da kasuwancin rogo na Nijeriya. Ya bayyana cewa, an amince a bayar da tallafin Dala Miliyan Biyar ga makarantar horar da dabarun kasuwanci ta Legas da abokan hulɗa wajen samar da hanyoyin bunƙasa tattalin arziki na noman rogo.
