Ɗan Afirka na farko da ya jagoranci Hukumar Kula da Ilimi da Al’adu da Kimiya ta Majalisar ɗinkin duniya wato UNESCO, Mukhtar Mbow ya rasu yana mai shekaru 103 a duniya.
Amadou Muhtar Mbow wanda ya jagoranci hukumar ta UNESCO daga shekarar 1974 zuwa 1987 jigo ne kuma abin koyi a ƙasar sa ta Senegal da ma nahiyar Afirka, wadda ya jajirce wajen samar da gagarumar ci gaba a ɓangarorin ilimi da zaman lafiya, kuma ya rasu ne yana mai shekaru 103, a cewar kamfanin dillancin labaran ƙasar Senegal APS.
Da jin labarin rasuwar Farfesa Amadou Muhtar Mbow shugaban ƙasar ta Senegal Bassirou Diomaye Faye ya gabatar da ta’ziyarsa a shafinsa na ɗ, yayin da ya bayyana shi a matsayin wani muhimmcin gimshiƙi a fagen ci gaban al’umma.
Shugaban ya ƙara da cewa Darakta janar ɗin jigo ne ga al’ummar Senegal wanda cike gurbinsa wani babban ƙalubale ga al’ummar ƙasar.
Sannan shima firaministan ƙasar Ousmane Sonko ya bayyana cewa Senegal ta yi gagarumin rashi ta fasihi kuma mutum mai karsashi a fagen tattali da kuma raya al’adu na gargajiya da aka san al’umma da su, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga ci gaban ƙasar da ma nahiyar Afirka bakiɗayan ta.
Darakta janar ta hukumar ta UNESCO Audrey Azoulay ta karrama Mbow bisa na mijin ƙoƙarinsa da kuma yadda ya bar baya da kyau daga irin ci gaban da ya samar a shugabancin hukumar ta Majalisar ɗinkin Duniya.
Mbow shi ne ɗan Afirka na farko da ya jagoranci wata hukuma ta ƙasa da ƙasa, wanda ya kasance abin koyi kuma cikakken haziki mai son ci gaban al’umma, ya kuma bar tarihi mai zurfi a cibiyar ta UNESCO ta hanyar kare buƙatar haɗin kai da daidaito tsakanin al’ummomi da al’adu. RFI.
