Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Daraktar sashen koyon sana’o’i wato Centre For Entrepreneurship Studies a Turance na babbar jami’ar jihar Nasarawa dake garin Keffi, Misis Ruth Andah ta ce kawo yanzu sashin yana cigaba da cimma burin kafuwarsa wato na samar da ingantaccen ilimin sana’o’i daban-daban irin ta zamani wa ɗimbin ɗaliban jami’ar baki ɗaya.
Daraktar Misis Ruth Andah ta bayyana haka ne a lokacin da take tattaunaw da wakilinmu game da harkokin cibiyar a ofishin ta dake jami’ar ranar Talatar mako da ake ciki.
Ta ce a yanzu haka cibiyar ta koyar tare da yaye ɗalibai da dama waɗanda aka koyar da su sana’oi’n hannu daban-daban da suka haɗa da ɗinki da renon kaya da kafinta da kitso da gyarar kai da aski da ilimin kwamfuta da ƙere-ƙere da yadda ake sarrafa sabulun wanka da na wanki da wanki da guga irin ta zamani da dai sauransu da dama inda a yanzu haka waɗannan ɗaliban suna gudanar da sana’o’in da aka koyar musu ɗin a wurare daban-daban da suka tsinci kansu don dogara ga kansu.
Misis Ruth Andah wacce muƙaddashiyar Farfesa ce ta kuma yi amfani da damar inda ta yaba wa hangan nesa da mahukuntar jami’ar suka yi na kafa cibiyar don a cewar ta kawo yanzu ya tallafa wa ɗaliban da dama wajen ba su damar dogara ga kansu maimakon su riƙa jira ayyukan gwamnati bayan sun kammala karatunsu.
Har ila yau Misis Ruth Andah ta kuma yawa wa shugabar babbar jami’ar ta gwamnatin jihar ta yanzu wato Farfesa Sa’adatu Hassan Liman dangane da cikakken gudunmawa da tallafi da take bai wa cibiyar don cigaba da samar da ingantaccen sana’o’in wa ɗaliban inda ta ce tabbas cibiyar na ɗaya daga cikin fannonin jami’ar da shugabar ke bai wa fifiko a yanzu.
A ƙarshe sai daraktar cibiyar ta koyon sana’o’in na jami’ar Misis Ruth Andah ta kuma yi amfani da damar inda ta buƙaci duka ɗalibai dake koyon sana’o’in a yanzu su cigaba da nuna kwazo da aiki tukuru don a ƙarshe kwalliya ta biya kuɗin sabulu wato su samu ingantaccen ilimin sana’oin dabandaban don amfanar kansu inda ta kuma bukaci iyaye su rika turo ‘ya’yan su cibiyar kasancewa a yanzu sana’a ce ke rufe wa kowa asiri fiye da wasu ayyukan.
