Na yi nadamar rashin sayen Arsenal – Ɗangote

Spread the love

Attajirin nahiyar Afirka kuma shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya ce yanzu lokaci ya wuce da zai sayi ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal da ke Ingila, inda ya ce zai cigaba da zama mai goyon bayan ƙungiyar a duk lokacin da take wasa.

Ɗangote ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Bloomberg, inda ya ce yana kallon wasannin ƙungiyar sosai.

“A zantawarmu ta baya na ce da zarar na kammala aikin gina matatar man fetur ɗina zan koma batun sayan Arsenal. Amma yanzu lokacin wannan maganar ya wuce domin komai yanzu ya yi tsada, sannan yanzu ƙungiyar tana ƙoƙari sosai, amma a wancan lokacin da na yi maganar ƙungiyar ba ta kan ganiya.”

Da aka tambaye shi ko ya yi da-na-sanin rashin sayan ƙungiyar a wancan lokacin, sai ya ce, “gaskiya na yi da-na-sani, amma kuma a lokacin na fi buƙatar kuɗin wajen kammala aikin da na ɗauko na gina matatar man fatur ɗin nan sama da sayan Arsenal ɗin. Da na saya ƙungiyar a lokacin a kan kuɗi Dala miliyan 2, amma kuma wataƙila da ban kammala aikin matatar ba. A lokacin zaɓi ne ko dai in kammala aikin gina matatar, ko kuma in saya Arsenal.”

A shekarar 2020 ne Ɗangote ya bayyana ƙudurinsa na sayan ƙungiyar ta Arsenal da zarar ya kammala aikinsa na gina matatar men fetur.

By ukarofi