Tinubu ya miƙa wa Majalisa ƙudiri huɗu na gyare-gyaren haraji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya rubuta wa Majalisar ƙasa ƙudiri guda huɗu da suka shafi lamarin haraji don yin nazari da kuma tabbatar da su.

Kakakin Majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya karanta ƙudirin inda ya ce an tsara su ne la’akari da gyare-gyare da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi.

Ƙudiri huɗun sune; ƙudirin haraji ta ƙasa na

2024, ƙudirin sanya haraji, ƙudirin samar da hukumar haraji ta ƙasa da kuma ƙudirin samar da hukumar haɗaka ta haraji.

Ƙudirin farko zai yi aiki ne wajen samar da tsarin gudanar da harkokin tattara haraji bisa salo na gama-gari.

Sai na biyu wanda shi ne zai kula da bin hanyoyin da doka ta tanadar wajen tsarin kula da harkokin haraji a Nijeriya.

Na ukun zai bada damar samar da hukumar kula da haraji ta ƙasa ƙarƙashin dokar hukumar tattara haraji ta ƙasa.

Na ƙarshen kuma zai kula da ɓangaren shari’a game da lamuran haraji wanda zai ke magance matsalolin da suka shafi ɓangaren.

Tinubu ya bayyana cewe, waɗannan tsare-tsaren za su inganta harkokin ƙuɗaɗen masana’antun Nijeriya da suka yi dai-dai da manufofin ci-gaba da gwamnatinsa ke ƙoƙarin samar wa ƙasa.

By Babaji