Kotu ta haramta wa VIO tsayar da motoci da tsare su

Daga BELLO A. BABAJI

Wata babbar kotu da ke Abuja, ta aika wa hukumar kula da zirga-zirgar motoci (VIO) saƙon umarnin dakatar da ita daga tsayar da motoci a kan hanya da tsare su a ofishinsu da kuma cin tarar direbobi.

Mai Shari’a Nkeonye Evelyn Maha ta bayyana hakan a lokacin da ta ke hukunci kan ƙara mai lamba kamar haka; FHC/ABJ/CS/1695/2023, inda ta ce jami’an hukumar ba su da ikon karɓe motoci ko sanya tara masu tsauri ga direbobi.

Waɗanda aka zayyano a matsayin masu kare ƙarar sune; Daraktan hukumar sufurin motoci, Area Kwamanda, ministan Abuja da sauran su.

Mai shari’ar ta ce, babu wata doka da ta bai wa jami’an damar karɓewa ko cin tara ga motoci da direbobinsu.

Ta kuma ce yin ɗaya daga cikin ababen da aka haramta, tauye haƙƙin ƴancin al’ummar ƙasa ne ba tare da sahalewar doka ba.

Kawo yanzu VIO ba ta ce komai ba game da batun yayin da aka yi hukuncin.