
Daga BELLO A. BABAJI
Shirin taron kasuwancin finafinan Afrika na yarukan Kano (KILAF), ya ayyana finafinai 57 da ka iya samun lambobin yabo a bajekoli na 2024 da za a yi ranar 30 ga watan Nuwamba a Kano.
Cikin wata hira da manema labarai da Shugaban KILAF, Malam Abdulkareem Mohammed, ya ce taron wanda shi ne karo na bakwai, an samu finafinai 57 cikin 510 da aka fitar a duniya waɗanda suka fito daga ƙasashe 66 inda 35 ƙasashe ne na Nahiyar Afirka.
Ya kuma bayyana cewa, daga finafinan 57 da suka fito daga ƙasashe 16, kowane ɗaya daga cikin su ka iya lashe wani daga cikin lambobin yabo 17 na taron.
Shugaban ya ce, za a shafe kwanaki biyar ne ana gudanar da taron kasancewar mutane daga ƙasashe daban-daban za su halarta.
An fara irini taron ne a shekarar 2018 don inganta harkokin masana’antun finafinan Afrika a idon duniya.
