Lakcar ƙasa-da-ƙasa ta NAN: Babban Hafsan Tsaro ya jaddada muhimmancin haɗaka a magance matsalolin Sahel

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba, 2024 ne jaridar ‘News Agency Nigeria’ ta yi taron shekara-shekara na ƙasa-da-ƙasa karo na farko a cibiyar albarkatun rundunar soji da ke Abuja.

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa a yayin taron, ya yi jawabin ƙaruwar taɓarɓarewar al’amura a shiyyar Sahel inda ya buƙaci Nijeriya da haɗin-gwiwar ƙwararru a fagen tsaro su haɗe kai wajen kawo ƙarshen rashin tsaro a yankin.

Ya ce, lamarin lalacewar harkar tsaro a Sahel ya samo asali ne daga rashin ingantaccen shugabanci, wariya ga harkokin tattali da kuma rushewar gwamnatin Libya a shekarar 2011.

Janar Musa ya kuma bayyana tsauraran ƙalubalen da Nijeriya da maƙoftanta ke fuskanta musamman ga samuwar ƙungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram da ISWAP waɗanda suka yi sanadiyyar ɗaiɗaita ƙauyuka da miliyoyin mutane.

Akan haka ne rundunar soji ta yi aiki da jami’an haɗaka na MNJTF don magance matsalolin tsaro da dawo da zaman lafiya a shiyyar wanda duk da hakan haƙa ba ta cimma ruwa ba, ya na mai kira da a fitar da salo iri-iri da ka iya daƙile ta’addanci da matsalolin tattali.

Ya nemi gwamnatoci da ƙungiyoyi masu zaman kansu da saura masu-ruwa-da-tsaki na ƙasashe su samar da hanyoyin magance matsalolin na dindindin wanda hakan ne kaɗai ne zai iya bada damar samar da ci-gaba a yankin baki ɗaya.

By Babaji