Ƙarancin fetur ya sa NNPCL rufe shafin sayen mansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ana hasashen ƴan Nijeriya za su fuskanci matsalar ƙarancin man fetur na ba da jimawa ba sakamakon samun tseko da ƴan kasuwa ke fuskanta dakon fetur bayan da kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya rufe shafinsa na sayen mai.

Mai magana da yawun ƙungiyar ƴan kasuwar fetur ta Ƙasa, Chinedu Okadike ya faɗi hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba inda ya ce ƴan kasuwa na da tikiti 2,000 na sayen fetur da adadinsa ya kai lita 45,000.

Ya ce, rufe shafin ka iya shafar yalwar mai a cikin al’ummar Nijeriya, ya na mai cewa kawo yanzu ba su da tabbacin nawa ne farashin man.

Yayin tsokaci game da lamarin, Kakakin NNPCL, Olufemi Soneye ya tabbatar da batun rufe shafin inda ya ce a halin yanzu kamfanin na aiki don ganin an shawo kan matsalar.

Ya ce, an yi hakan ne don kar a karɓi kuɗaɗen ƴan kasuwa na tsawon lokaci ba tare da ba su abin da suka saya ba.

Ya ƙara da cewa, nan ba jimawa ba za a sake buɗe shafin.

A halin yanzu dai al’umma a Nijeriya na sayen litar fetur a tsakanin N950 da N1,100 inda a wasu wuraren ma ya kan haura hakan.

By Babaji