Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Shugaban Hukumar ƙidaya ta jihar Kano, Dakta Aminu Ibrahim Tsayawa ya bayyana cewa shirin yin ƙidaya ga al’ummar ƙasar nan na nan tafe nan ba da daɗewa ba.
Ya bayyana haka ne a Kano yayin da yake zantawa da ‘yan jarida a cikin makon nan.
Ya ce jama’ar jihar Kano su zama a cikin shirin ƙidayar, domin da sanin yawansu ne za su samu kaso da ya dace da ita na samun rabon albarkatun ƙasa da gwamnatin tarayya.
Ya ce duk da dai ba a kai ga sanya takamaimai ranar da za a yi ƙidayar ba, amma an gama tattara dukkan abubuwa da ake da buƙata na aikin ƙidayar tuni ma kayan sun zo jihar Kano.
Ya ce yanzu duk abubuwa da ake na cigaban ƙasa ana yinsa ne bisa hasashen yawan al’umma, saboda babu tabbacin yawan al’umma wannan tasa gwamnati ganin lallai ya kamata a zo a yi ƙidayar.
Ya ce tun a shekara ta 2020 ake ta shirye-shirye za a yi ƙidayar a 2023 amma duba da wani akasi da aka samu ya sa ba a iya yin ƙidayar ba, “domin har an sai kayayyaki kowace jiha ma an tura mata har da nan jihar Kano, muhimman kayayyaki da za a yi amfani da su suna ajiye a babban bankin ƙasa.”
Dakta Aminu Tsayawa ya yi nuni da cewa akwai hasashen Kano tafi kowace jiha a ƙasar nan yawan jama’a amma idan ba a samu cikakkiyar haɗin kai na al’ummar jihar ba za a iya samun matsala domin a cewarsa gwamnati na amfani da alƙaluman ƙidaya wajen bunƙasa arziƙi da rabon arziƙin ƙasa.
Tsayawa ya ce sai an tashi tsaye sosai an faɗakar da jama’a muhimmancin amfanin yin ƙidaya saboda idan lokaci ya yi kowa zai fito ya bada haɗin kai a yi ƙidaya ba tare da an tsallake kowa ba.
