Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 118 da kama 97

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hedkwatar Tsaron ƙasa (DHQ) ta ce jami’ai a sassa daban-daban na Nijeriya sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda 118 tare da kama kama wasu 97.

Ta ce, jami’an sun kuma kama wasu mutum 18 da laifin satar mai da kuma ceto mutane 96 da aka yi garkuwa da su.

Daraktan Labaran DHQ, Manjo-Janar Edward Buba cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce jami’an sun bayyana adadin kuɗin man, wanda suka ce ya kai sama da Naira Miliyan 793.2.

Ya ce, jami’an na cigaba da hallaka ƴan ta’adda da jagororinsu a atisayen da su ke gudanarwa a sassa daban-daban na faɗin ƙasar.

Ya ƙara da cewa, jami’an sun kuma ƙwato manyan makamai guda 87 da alburusai 2,244 daga ƴan ta’adda.

Kazalika, a yankin Nija-Delta, jami’an sun gano tare da tarwatsa ramuka huɗu na fakewar ɓarayi, jiragen ruwa 48 da masu gudu 3, da duro guda 156 da kuma tankunan ajiya 34.

By Babaji