Rundunar ƴan sanda za ta tsame hannunta a zaɓen ƙananan hukumomin Ribas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sandan Jihar Ribas ta sanar da cewa za ta tsame hannunta a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi ranar Asabar.

Kakakin rundunar, SP Grace Iringe-Koko ta faɗi hakan wa manema labarai a Fatakwal, babban birnin jihar a ranar Juma’a inda ta ce an yi hukuncin ne sakamakon umarnin babbar kotun tarayya.

Ta ce, a yanzu haka rundunar ta fara janye jami’anta daga harkokin zaɓen, ta na mai kira ga sauran hukumomi su kula da hukuncin da kotun ta yi don tabbatar da kiyaye doka.

Ta kuma shawarci duk wanda ke da ja akan hukuncin kotun, ya ɗauki matakin doka gabannin zaɓen.

Haka ma, ta bada tabbacin jami’anta za su kasance a ankare duk da cewa ba sa cikin masu aiki kai-tsaye a zaɓen.

A ranar 39 ga watan Satumba ne kotun ta hana hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) bai wa hukumar zaɓen jihar (RSIEC) rijistar masu zaɓe sakamakon rashin bin dokar rijistar zaɓe da RSIEC ta yi.

Baya ga haka ne kotun ta umarci ƴan sanda da ƴan sandan farin kaya na jihar su ƙaurace wa shiga zaɓen.

By Babaji