Rundunar soja za ta binciki tsohon kwamandanta na Kano kan zargin sama da faɗi da kuɗin ƙananan sojoji

Spread the love

Hedikwatar sojojin Nijeriya ta fara gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa tsohon kwamandan Birged na 3 a Kano, Birgediya Janar M.A. Sadiq.

Wakilinmu ya tattaro cewa an sallami janar ɗin ne biyo bayan tuhumar da ake masa na ƙin biyan wasu haƙƙoƙin da ke ƙarƙashinsa, tare da wasu zarge-zarge na almundahana a lokacin da yake riƙe da muƙamin kwamanda.

Wata majiya ta soji ta shaida wa wakilinmu cewa Janar ɗin na ci gaba da zama a tsare kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Da aka tuntuɓi daraktan yaɗa labarai na tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya miƙa wa wakilinmu ga daraktan hulɗa da jama’a na rundunar.

Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojojin, Manjo Janar Onyema Nwachukwu Onyema, ya ce a na gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Onyema ya ce, “Rundunar sojin Najeriya, kasancewarta cibiya ce mai cin gashin kanta da aka kafa a kan ginshiƙin ɗa’a, adalci, da riƙon amana, ba ta da jure rashin ɗa’a, don haka ba za ta lamunci duk wani nau’i na rashin ɗa’a ko ayyuka na haram da kuma rashin aiki da zai iya kawo cikas ga ƙa’idojin aiki na rundunar.

Ya kuma ba da tabbacin cewa za a yi bincike sosai a kan zargin sannan za a ɗauki matakin da ya dace idan aka same shi da laifi.

Muna ba da tabbacin cewa tsarin zai kasance na gaskiya, ba son kai, domin hakan ya yi daidai da ƙa’idojin mu.

By ukarofi