Gwamnatin Tarayya ta wanke kanta a ƙarin farashin fetur, ta ce daga kasuwar duniya ne

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta nesanta kanta daga batun ƙarin farashin litar fetur, ta ce hakan ya faru ne sakamakon sauye-sauye da ake samu a kasuwannin duniya da kuma hukunci da kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya yi.

A wata hira da jaridar Daily Trust, Ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Mohammed Idris, ya ce gwamnatin tarayya ba ta bai wa NNPCL umarnin haka ba, ya na mai cewa hakan na faruwa ne sakamakon jujjuyawar kasuwannin duniya da kuma rashin ikon kamfanin na bada farashin fetur la’akari da dokar sayar da man fetur ta ƙasa.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa, gwamnati na ƙoƙari wajen inganta ɓangarorin lafiya, ilimi, tsaro da sauran ababen more rayuwa a ƙarƙashin tallafin fetur da aka cire.

Ya ƙara da batun zuba hannu da gwamnatin tarayya ta yi a tsarin iskar gas na CNG a matsayin mafita ga man fetur.

By Babaji