NLC ta buƙaci a gaggauta cire ƙarin da aka yi wa farashin fetur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC ta nemi a cire ƙarin da aka yi ga kuɗin litar fetur a Nijeriya, ta ce hakan na ƙara talauta al’umma.

A ranar Laraba ne kamfanin man NNPCL ya sanar da sabon farashin litar fetur wanda ya koma daga N898 zuwa sama da N1,030.

Shugaban NLC, Joe Ajaero ya bayyana takaicinsa ganin yadda farashin fetur ke ƙaruwa a duk wata tare da cewa ba a kai ga zartar da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata ba a ƙasar.

Cikin wata sanarwa da NLC ta fitar, Ajaero ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda NNPCL ke tsara yadda farashin fetur ke kasancewa a Nijeriya ba tare da la’akari da halin matsi da al’umma ke ciki ba a ƙasa.

Ya kuma ƙalubalanci gwamnati ta nuna ci-gaban da aka samu ta fuskar tattali da wasu nau’ukan ci-gaba in ban da irin hakan da kuma tsarin bada tallafi.

Kazalika, Ajaero ya bayyana hakan a matsayin abin da zai ƙara gefa al’umma cikin talauci da kuma rasa ayyukansu a ƙarƙashin illar da hakan zai haifar.

A sakamakon haka, shugaban ƙungiyar ya ke kira ga gwamnati ta gaggauta mayar da farashin yadda ya ke, ya na mai cewa ƙarin da aka yi a baya bai bada sakamako na ci-gaba da aka yi tsammani ba.

By Babaji