Rundunar ‘yan sandan Kano ta cafke mutum uku da ake zargin sun kashe matashi

Spread the love

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da kashe wani matashi mai suna Ɗahiru Musa ɗan shekaru 32 da haihuwa a unguwar Ɗorayi Quarters Kano.

Waɗanda ake zargin sun yi wa Musa ƙarya ne, inda suka sanya masa guba, sannan suka ƙona gawarsa da nufin lalata shaida.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kano.

Haruna ya bayyana cewa Waɗanda ake zargin, Aliyu Adamu mai shekaru 22, Mubarak Abdulsalam mai shekaru 20 da Sadiq Sunusi mai shekaru 19. A halin yanzu suna hannun ‘yan sanda.

“A ranar 29 ga Satumba, 2024, da misalin ƙarfe 7:30 na yamma, wani mazaunin unguwar Ɗorayi Quarters, Kano, ya kai ƙarar ɓacewar ɗan uwansa Ɗahiru Musa. Ya tuhumi Aliyu Adamu, mai shekaru 22, daga Gaida ‘Yan ƙusa Quarters, ƙaramar hukumar Kumbotso, jihar Kano, wanda shi ne mutum na ƙarshe da ya yi hulɗa da marigayin,” ya bayyana.

Bayan wannan rahoto, jami’an tsaro sun yi gaggawar fara bincike tare da kama Adamu washe gari. A yayin da ake yi masa tambayoyi, Adamu ya amsa laifin haɗa baki da abokinsa, Mubarak Abdulsalam, domin su kai Musa gidansa bisa zargin cewa za su tattauna batun filaye.

Haruna ya ci gaba da cewa, “Sun ba shi abinci mai guba, kuma da ya sume, sai suka daɓa masa wuƙa har ya mutu.”
“Sun naɗe gawar a cikin buhu su ka jefar a wani gini da bai kammala ba kusa da gidan Adamu.”

Binciken ya ci gaba da cewa bayan kama Adamu, Abdulsalam ya haɗa baki da wani mai suna Sadiq Sunusi, inda suka ƙona gawar Musa da fetur a kokarin lalata duk wata shaida da ta rage.

Kwamishinan ‘yan sanda, Salman Garba, ya yabawa jama’a bisa rawar da suka taka wajen bayar da muhimman bayanai da suka kai ga kama mutanen. Ya kuma shawarci mazauna yankin da su kasance cikin taka tsan-tsan, musamman wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci a wuraren da ba a san su ba.

By ukarofi