Kotu ta jaddada dakatar da Aminu Ado Bayero daga gyara Fadar Nassarawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wata babbar kotun tarayya da ke Jihar Kano ta jaddada dakatar da Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero daga aikin gyaran ƙaramar Fadar Nassarawa.

Gwamnatin jihar Kano, Antoni Janar na jihar da kuma Majalisar Masarautar Kano suka shigar da ƙarar dakatarwar ta hannun wani babban lauyan Nijeriya (SAN), Rilwanu Umar.

A yayin hukuncinta, Alƙalin Alƙalan Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki ta tabbatar da buƙatar waɗanda suka shigar da ƙarar tare da umartar a mayar da ƙarar zuwa babbar kotu ta 15 don cigaba da sauraro.

Haka nan, a cikin takardar, masu shigar da ƙarar sun nemi kotun ta bayyana Fadar Nassarawa a matsayin mallakar jihar da Majalisar Masarauta ba na wanda aka shigar da ƙarar akan sa ba.

A ranar 13 ga watan Satumba ne, kotun ta dakatar da Sarki Aminu Ado daga cigaba da aikin gyaran Fadar ko kuma yin kowacce irin kwaskwarima, wanda a yanzu ma ta sake yi.

By Babaji