Daga UMAR GARBA a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta sha alwashin rabawa waɗanda ambaliyar ruwa na bana ya rutsa da su, tallafin kuɗi Naira bilyan biyu.
Gwamnan Jihar Dikko Umar Raɗɗa ne ya bayyana haka a yayin ƙaddamar da rabon tallafin shinkafa ga wasu daga cikin al’ummar jihar.
Bankin masana’antu (BOI) ne ya bada tallafin shinkafar, inda aka raba sama da buhu 2,000 ga mabuƙata a ƙarshen makon nan.
Raɗɗa ya ce, an ware Naira biliyan biyu ne domin tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa don sake gina gidajensu da kuma kasuwancinsu.
Yayin da gwamnan ke yabawa bankin masana’antu kan tallafin shinkafar, Raɗɗa ya yi kira ga ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da su tallafa wa jihar da abinci da sauran kayayyaki.
Ya kuma yi kira ga waxanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kayayyakin da aka tallafa masu da shi yadda ya dace, su kuma guji sayar da kayan tallafin.
Rabon shinkafar wanda hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) ke kula da shi, an tsara shi ne don tallafawa ‘yan gudun hijira da mata da kuma masu buƙata ta musamman a faɗin ƙananan hukumomi 34 na jihar.
Babbar sakatariyar hukumar ta SEMA, Binta Ɗangani ta ce an zaɓo waɗanda za su ci gajiyar shirin daga yankunan da lamarin ya shafa.
