Amaechi ya fusata kan yadda ‘yan Nijeriya ba su tashi tsaye ba kan jefa su cikin tsadar rayuwa

Spread the love

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana rashin jin daɗinsa da yadda jama’a ke nuna halin ko in kula dangane da matsanancin matsin tattalin arziki.

Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na ABN TV, Amaechi ya yi tambaya kan dalilin da ya sa ‘yan Najeriya ba su nuna fushin su ba, domin ya ce,abubuwa sun yi tsadar da shi kanshi yanzu fama yake da har ta kai ba shi da kuɗin man dizal.

“Ina fushi da ’yan ƙasa. Na sha faɗin hakan. Za su ga mutane suna sace masu kuɗi suna talauta su, amm ba za su iya masu komai ba.

“Ya kamata mutane su yi fushi. Kamata ya yi a yi zanga-zanga. Ba ma zanga-zangar adawa da kowa ba amma ga ’yan siyasa cewa ‘ba za mu zaɓe ku ba.

“Dubi abin da ya faru a jihar Edo. Shin wani ɗan siyasa ya kamata ya yi yaƙin neman zaɓe a Edo? Ya yi tambaya, inda ya ƙara da cewa ‘yan ƙasar su ƙara ɗaukar tsauraran matakai kan ‘yan siyasa. “Ya kamata mutane su yi fushi. Kamata ya yi a yi zanga-zanga. Ba ma zanga-zangar adawa da kowa ba amma ga ’yan siyasa cewa ‘ba za mu zaɓe ku’ ba. Ba za a yi zaɓe a jiharmu ba.”

Ya kuma jaddada cewa ‘yan Najeriya su tashi tsaye su aika da sako mai ƙarfi, ba ta hanyar tashin hankali ba, sai dai su hana su shiga zaɓe har sai an fifita musu buƙatunsu.

By ukarofi