Daga IBRAHIM ALHASSAN a Kaduna
Rukunin Kamfanonin Qausain ‘Group of Companies”, Mamallakin Gidan Talabijin Qausain Tɓ ya yi wasu muhimman naɗe-naɗe na manyan shugabannin da za su ja ragamar kamfanin da suka haɗa da Shugaban Amintattu da Manyan Daraktoci.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Rukunin Kamfanonin Qausain, Alhaji Nasir Musa Idris (Albani Agege) ya sanya wa hannu a ranar Litinin, ya bayyana cewa Hukumar Gudanarwar Qausain ta amince da muƙaman ne a yayin Babban Taron Daraktocin Kamfanin da ya gudana a ranar Juma’ar da ta gabata a Kaduna.
An naɗa Tsohon Gwamnan Mulkin Soja na Jihar Kano, Kanar Sani Bello (Mai Ritaya) a matsayin Shugaban Kwamitin Amintattu na Kamfanin, yayin da Tsohon Ministan Sadarwa kuma Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin Babban Darakta na Qashin-Kai.
Sauran sune ƙwararren ɗan Jarida kuma Tsohon Ma’aikacin BBC Hausa, Ahmad Abba Abdullahi a matsayin Babban Darakta na Qashin-Kai, yayin da Shahararren Jarumin Fina-finan Kannywood kuma Mawaƙin Hausa, Adam Zango ya zama Babban Daraktan kamfanin.
A daidai lokacin da yake taya sababbin shugabannin murnar wannan naɗi, Babban Shugaban Rukunin Kamfanonin Qausain Malam Nasir Albani ya kuma yi kira gare su da su yi amfani da ƙwarewa da gogewarsu a ɓangarori daban-daban domin kai Kamfanin zuwa babban matakin da ya dace.
Kanar Sani Bello zai jagoranci Kwamitin Amintattu na Kamfanin ne na tsawon shekaru huɗu a bisa tanadin dokar kamfanoni na ‘Companies and Allied Matters Act’. Aikace-aikacen nasa za su Ƙunshi sanya ido akan wanzar da al’amura da cigaban Kamfanin da Manyan Daraktocin ke gudanarwa.
Kazalika sabon matsayin na Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin Babban Darakta Na ƙashin-Kai zai shafi kula da nagartar aikace-aikacen kamfanin waɗanda suka dace da zamani. Sannan kuma babban mai nusar da kamfanin game da ƙirƙira da kaucewa dukkan faɗawa cikin garari da koma-baya.
Sannan Muamin Ahmad Abba Abdullahi wanda ya shafe shekaru 28 yana gabatar da shirye-shiryen BBC Hausa zai maida hankali ne akan ƙololuwar nagartar aikace-aikacen jarida, bin ƙa’idar aikin yana shirye-shirye na ciki da wajen qasa.
Sai kuma naɗin Jarumin Fina-finan Kannywood Adam A. Zango wanda Hukumar Qausain ɗin ta ce zai fara aiki anan take, zai ja ragamar kamfanin ne a matsayin Babban Darakta.
Kazalika sanarwar ta ƙara da cewa an yi la’akari ne da ƙwarewarsa a ɓangaren isar da saƙo ga al’umma, zai kuma jagoranci Daraktocin Kamfanin wajen yaɗa nagartattun shirye-shiryen da za su cigaba da ilmantar da al’umma da faɗakarwa cikin nishaɗi da kuma bunƙasa harkokin tallace-tallace.
