Ko gobe mutane za su karɓi taliya su yi zaɓe saboda yunwa – Bello Guiwa

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Dakta M.B Abubakar, wanda aka fi sani da Bello Guiwa, ba ya buƙatar gabatarwa, musamman a Jahar Sakkwato da maƙwaftanta. Mutum ne da ya ga jiya da kuma yau a fannin siyasa da al’amurran yau da kullum.

Jajirtaccen mutum da dubattan mutane suka jima suna cin moriyar sa ta fuskoki da dama, kuma ɗaya daga cikin mutanen da jama’a ke hasashen da za a same su a madafun iko zai kawo sauyi mai matuƙar tasiri ga talakan Jahar Sakkwato. 

A  tattaunawarsa da jaridar Blueprint Manhaja, mai karatu zai samu muhimman batutuwa da suka shafi gwamnati da kuma sha’anin tsaro. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Dakta Bello Guiwa;

MANHAJA: Ko ya ka ke kallon siyasa a Jahar Sakkwato a yanzu da kuma yadda take a baya?

BELLO GUIWA: Auzu bii llahi sami’ul alim, minan shaiɗanin rajim. Bismillahi rahmananin Rahim. Wa salalallahu alal naibiyun karim. Aisha idan ki ka ce siyasa a Jahar Sakkwato, zan iya cewa gaskiya mu ba siyasa muke yi a Jahar Sakkwato ba. Don haka ban san irin amsar da ta dace da tambayarki ba, saboda dai sai ana yin siyasar ne za ka iya faɗar yadda take.

Za mu so ƙarin haske kan amsar da ka bayar. Shin kana maganar yanzu ba lokacin siyasa ba ne ko kuwa ba a yin siyasa gabaɗaya a jahar?

Ina nufin kwata-kwata ba siyasar ake yi ba. Da farko dai abinda ake cewa siyasa, a fara ta kan jam’iyya ita kanta, tsare-tsare da manufofinta, sai kuma sahihin zaɓe, wato mutane su zaɓi ɗan takarar da suke so ya zama mai wakiltar ita jam’iyyar a babban zaɓe. Sai kuma idan aka zo zaɓen jama’a su zaɓi wanda suke so ya shugabance su. Wannan ita ce ake cewa siyasa.

To mu a nan Sakkwato ba haka ake yi ba. Abu na farko, ni ban san wani mutum ɗaya a Sakkwato da yake siyan fom a jam’iyya don manufofin jam’iyyar ba, maimakon haka ana shiga ne don wane ita yake don haka ni ma ita zan yi, ko ina samun wani abu don haka ita zan yi, wato dai zai shiga don tasa biyan buƙata, amma ba don manufofi da aƙidu na ita jam’iyyar ba.

Wannan ne ya sa a yanzu babu wata jam’iyya da za a iya kira jam’iyya, asalima a Nijeriya bakiɗaya babu jam’iyya ko ɗaya. Domin duk jam’iyyar da ka ɗauko ba ta da wata manufa. Dalilin kenan da ke sa yau kana wagga jam’iyyar, gobe kana iya komawa wata. Saboda dama ba su da manufofi, don haka kai da ka zo ba manufar ta kawo ka ba. Ana taruwa ne kwai a jam’iyya a yi zaɓe, a saci kuɗin gwamanati.

Abu na biyu daga ababen da na ambata, wato tsayar da ɗan takara wanda ake so, to mafi yawa daga ‘yan takarar da ake tsayarwa yanzu a Jahar Sakkwato jama’a ba su son su, amma da ƙarfi da yaji wasu ke tursasawa, su tsaishe su. Saboda ƙarfin da suke da shi. To kin ga duk inda ka cusa ma mutane wani, wanda ba su son shi, ba za a kira wannan siyasa ba.

Abu na uku, zaɓen ma, wato babban zaɓe idan aka zo, ko duk Jahar Sakkwato za ta taru ta zaɓe ka, Hukumar Zaɓe, da sojoji da ‘yan sanda, za su iya taruwa su murɗe zaɓen, su ba wa wanda suke so.

Da waɗannan ababe uku da na faɗa, zai fahimatar da a Sakkwato ba a siyasa. Duk wanda ki ka gani  bi sa wani muƙami a yanzu a Jahar Sakkwato, to babu wanda mutane suka zaɓa da kansu. An hau ne da ƙarfi da yaji.

To zancen yadda mulki da siyasa yake a Jahar Sakkwato babu ta, domin wanda aka zaɓa ne bisa ra’ayi ake masa zancen siyasa da mulki.

Wannan na ɗaya daga dalilin da ya sa ki ke ganin ake wa mutane mulkin kama-karya. Shuwagabanni na yadda suka ga dama. Saboda sun san ba mutanen da suke mulka ne suka aza su ba.

Shi ya sa duk ƙarya ce, babu wata dimukaraɗɗiya a Nijeriya. Wanda ya fi wani garfi ne ake yi.

Yallaɓai bari mu koma ɓangaren matsalar tsaro wanda a yanzu kusan in ce ita ce ta fi addabar mutanen Nijeriya, musamman ma shiyoyin Katina, Zamfara da Sakkwato. A matsayinka na wanda ya ga jiya ya ga yau akan harkar al’amurran da suka shafi siyasa da rayuwa bakiɗaya. Waɗanne irin hanyoyi ka ke ganin za a iya bi don kawar da matsalar rashin tsaro musamman a yankunan Zamfara da Sakkwato?

Aisha, ba za a iya magance matsalar tsaro ba a Nijeriya, saboda duk ƙarya ce. Abinda aka ƙirƙiro da gangan, to abinda aka shirya ya za a yi tunanin ana son ya tafi. Wannan matsala da ki ka ga ta addabi Zamfara zuwa nan ba fa wani abu ba ne inba zinari ba. Saboda kawai ana so a haƙo zinari ne, kuma manyan da su ake yi. Kuma kowa ya sani. Bari in ba ki misali da Sakkwato, yanzu akwai unguwa a Sakkwato wadda ‘yan daba da ‘yan kidinafin suka gina gidaje, suke zaune a cikinsu, kuma duk jami’in da a Sakkwato ya san su, ko ya san suna nan. Amma kullum faɗin ake ba a san inda suke ba. Kamar zancen Bello Turji da ake ta yi na ba a san inda yake ba. Wallahi ba wani sojoji da ke biɗar inda Bello Turji yake, don sun san inda yake. Kowane shugaba na ‘bandits’ an san inda yake an Nijeriya.

Yanzu Bello Turji ɗin nan, da wanda aka kashe Sububu, suna Facebook, suna Twitter, suna TikTok, suna Instagram, suna faɗin abinda suka ga dama. Kuma suna ta wayoyi suna abinda suke so. Amma wai ba a san inda suke ba. Amma yau da za ki ɓaci Remi Tinubu, wallahi duk inda ka ke Nijeriya, sai an yi ‘tracking’ ɗin ka an kamo ka. Kaga yadda dai aka kamo wanda ya zagi Aisha Buhari, kuma fa ba ma zagin nata ya yi ba yadda ake faɗa, cewa ya yi “ta hau kaya.” Kuma karya yake yi ba ta hau kayan ba?

Yau da za ka zagi wani insifecta na ‘yan sanda, duk inda ka ke sai sun kamo ka. Amma wai a ce ba a san inda ‘yan ta’adda suke ba. Saboda haka mutane ku farga, wannan wasan kwaikwayo ne kawai ake maku. Saboda su ke amfana da yin hakan. ɗauki misalin kuɗaɗen da ake ce mana ana kashewa a harkar tsaro, ke kinsan sun saɓa wa hankali. Kuma duk duniya ba inda ki ka ji ana haka, ace wai ga wasu jahillai, ƙauyawa, wai sun hana wa ƙasa zaman lafiya, kuma an rasa yadda za a yi da su.

Kin ga shugabannin nan namu, wallahi ba su san Allah ba, daga Musulman har kafiran. Idan har ‘yan Nijeriya dukka za su mutu ba abinda zai dame su, matuƙar bai shafe su da iyalansu da kuma burinsu ba. Don har yau ba ki ji wani abu da shugaban Nijeriya ya fasa yi ba don alhinin an yi kidinafin ɗin wasu mutanensa ko an kashe su ba. Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da su ka sa ƙasar ta fita ran ɗiyanta. Domin ƙasar ba ta son ‘yan ƙasar tata, don haka su ma ‘yan ƙasar ba sa son ƙasar.

Ko rashin son da ‘yan ƙasar ke yi wa ƙasar ne ya sa ba su damu da wanda zai mulke su ba, ta hanyar siyar da ƙuri’unsu?

Na san ana siyar da ƙuri’a, amma bari in tambaye ki Aisha, shin ba ki san dagangan ne ake talauta ‘yan Nijeriya ba? Ai ‘deliberate attempt’ ne don a tilastaka yin abinda ake so, ko ba ka so. Yanzu kali yanayin da Nijeriya take ciki yanzu. A tarihi ba a taɓa lokacin da aka shiga matsi a ƙasar nan kamar yanzu ba. Kowa abinda ya ci yake biɗa. To yanzu kina tsammanin yadda yunwa ta kai ma mutane koina. Ana zuba wa tafasa ruwan zafi a ci, wani ya kwana ya yini bai ci ba. Yanzu haka wallahi a yini ina samun saƙwannin mutum sama da 20 masu roƙona, don Allah in taimake shi, wallahi gida nai ba a ci abinci ba. To shi za a yi tsammanin a ba shi taliya gobe yaƙi yin zaɓe.

Menene laifin talaka idan ya kaɗa ƙuri’a aka ba shi taliya? Ai yunwa ce za ta kashe shi, kin ga ko dole ce za ta sa ya amsa. Kuma wannan yunwar deliberately aka sa ma mutane ita, domin Nijeriya ba ta da yunwa. To idan ba ki bada ƙuri’arki aka ba ki indomie ko taliya, ya za ki ciyar da iyalinki.

Ilimin ma da ya kamata a ba wa mutane na su daina siyar da ƙuri’a, su yi haƙuri, su zaɓi cancanta don a gyara masu goben su, to ilimin ma ka hana masu.

Kin je makarintinenmu? Ke taɓa ‘interɓiew’ da mallamanmu? Wallahi mallamanmu ba su san abinda suke ba, to bare ɗalibai. Wallahi graduate na sakandare a baya, ya fi ‘graduate’ na jami’a a yanzu. Yaro ya gama jami’a, ya je NYSC ya kasa cika fom na NYSC, ka tambaye yaro Course  ɗin da yakai, ka ce ya rubata shi ya kasa rubata sunan course ɗin da ya yi ya kasa. Yadda ake siyar da digiri, da NCE da sauransu har ya saɓa wa tunani. Kuma wannan na da alaƙa da yadda ita gwamanati ke yaudarar ma’aikatanta. Ka faro karatu tun daga naziri, firamare, sakandare zuwa jami’a, amma ba ka da ta cewa akan abinda gwamanati za ta biyaka, in ma ka yi sa’a ka samu aikin. Abinda za a biya shi ko shi karan kai nai ba ya isar sa, bare iyalinsa. Kinga komai zai iya yi.  

Saboda haka tilastawa talakawa aka yi karɓar taliya da Indomie su bada ƙuri’a. Ai in ka bar mutum da yunwa, to komai shina iya yi. Mutane na ta cewa wannan hali da aka shiga na matsin rayuwa ba wanda za a sake ba wa taliya ya zaɓi Tinubu. Na ce, ko gobe talakawa za su sake zaɓen Tinubu, saidai idan bai bada taliya da Indomie ba, don yunwa suke ji.

Ko akwai hanyoyin da ya kamata mutane su bi don samar wa kansu mafita?

Tabbas akwai. Ai randa Allah ya yi ki, ba ki taɓa jin al’umma ta lalace a ƙarƙashin shugabancin mutanen kirki ba. Sannan ba ki taɓa jin al’umma ta gyaru ƙarƙashin shugabancin mutanen banza ba. Duk sadda ake so al’umma ta samu cigaba, a kaucewa waɗannan matsalolin, to a zaɓi mutanen kirki. Ya kullum ba ku da aiki sai tsayar da mutane ‘yan iska, marasa mutunci, sannan ka yi tsammanin al’umma ta gyaru. kuma su shuwagabannin a kullum suka gama mulki sai su ɗauko waɗanda suka fi su lalacewa su sa. shi ya sa a kullum ake cewa gwara jiya da yau. Don haka ana iya gyara idan an so a yi gyara. A tsayar da mutanen kirki, masu iya gyara. A daina kawo ‘yan iska da ba abinda suke so sai su kwashi kuɗi su maida Dala su tara. Yanzu abinda gwamnoni ke yi kenan. Idan aka kawo alokeshon a tafi a canza su zuwa Dala a ɓoye.

Da yake ka yi zancen ka taɓa tsayawa takara, ko kana ganin ababen da ka fahimta da irin tafiyar da ka ga mutane na yi ko ya sare ma gwiwa ka ji ka daina sha’awar takara?

Ni ba sha’awar sake komawa takara ce ba ni da ba, ni duk yunƙurin da na yi, don na taɓa yunƙurin yin takarar gwamna, amma ban yi ba. Na taɓa takarar ɗan majalisa, amma wannan na yi, amma gaskiya abinda ya kashe min gwiwa, ‘system’ ɗin a ban yarda da shi ba, tsarin na fahimci ƙarya ce kawai aka shimfiɗa. Kamar dai bokon Nijeriya ne. To haka siyasar Nijeriya ta ke. Shugabancin Nijeriya ƙarya ce. Ba da gaske ba ne. kuma babu wanda ka nuhi nai da gaske. Ko dai ka yi irin na Buhari, kana son ka ci mulki don ka ci mutuncin waɗanda suka yi ma, ko kuma ka tara kuɗi, amma kuɗin ba su ishe ka ba, don haka ka ke son ka zama shugaba don ka ƙara tara kuɗi, don ka fi kowa kuɗi.

To wannan ce take faruwa a tamu Jahar. Yanzu idan kin taho Sakkwato, gwamnanmu bai da wata ajanda. Bai san ma don mi yake son ya za gwamna ba, kuma har ya zama gwamna bai ma san abinda dalilin da ya sa yake son zama gwamna ba, hasali ma har ya zama gamnan bai gama amincewa da shi ɗin gwamna na ba. Shi ya sa har yanzu da ya kai kusan shekara biyu da zama gwamna bai da aiki sai ɓacin gwamnatin baya. Maimakon ya mayar da hankali ga aiki kafin ya sauka shi ma a zage shi, tunda shi ma zagin nasa za a yi in ya sauka.

Amma ka koma ba abinda ka ke tunani sai yadda za ka yi ramuwar gayya. Ya za ka yi ka ci mutuncin wane tunda bai yi ka ba, ko ya za ka tozarta wane tunda bai yi ka ba. Shi ya sa na ce, ma ki shugabanci ya lalace, shi ya sa na ce, ban ganin hikima, ban ganin sha’awa tai. Ban ganin sha’awar gwamnan Sakkwato, kuma wanda zai ci nan gaba ma bai birge ni. Ban ganin don ka zama gwamna ka zama wata tsiya.

To yanzu a ce ka samu masu aƙida irin taka, waɗanda za ka iya amincewa tabban-tabban naka ra’ayi ko aƙida a siyasa ya zo daidai da irin nasu, da kuma irin manufofin da ka ke da su ga al’umma iri ɗaya. Shin akwai yiwuwar za ka amince ka fito takara?

Wannan kuma ai wajibi ne, don a taimaki al’umma su fito daga wannnan bala’in da suke ciki. Idan ka samu irin wannan damar ko ƙarfin, idan ka ƙi, to kamata ya yi ma a halbe ka, domin nauyi ne da yake kanka, da ya kamata ka sa hannunka, da ƙafarka, da komai naka, don yaƙin tabbatar da an tsamo mutane daga halin matsi da tsoro da suke ciki.

Kuma abinda mutane ba su gane ba, wato ita siyasa ba ta tsaya a iya cinye zaɓe ba. Ni yanzu da irin waɗannan mutane da ki ka ambata yanzu, wallahi ko an rubuta a goshi aka ce ba mu cin zaɓe, wallahi ni zan yi takarar, saboda na san na yi wani yunƙuri na tsamo mutane daga halin da ake ciki.

By ukarofi