Jam’iyyar PDP ta naɗa Ahmed Yayari wanda shine ma’ajin jam’iyyar a matsayin sabon shugaban ta na riƙon ƙwarya bayan dakatar da Umar Damagun da wani tsagin kwamitin gudnarwar jam’iyyar ya yi.
Sanarwa ta fito a wata takarda wadda sakataren jam’iyyar Hon. Debo Ologunagba ya sanya wa hannu a ranar Juma’a a Abuja.
Sanarwar ta bayyana Yayari Ahmed a matsayin sabon shugaban riƙon ƙwarya kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya bada damar yin hakan.
Kwamitin ya roƙi mambobi da su haɗe kansu kuma su maida hankali ga taron kwamitin gudanarwa da ake sa ran za ayi 24 ga watan Oktoba 2024.
Sannan kwamitin ƴan majalisu na jam’iyyar su ma sun amince da dakatar da Damagun da kuma naɗin Yayari Ahmed.
