Ya cinna wa sabuwar amaryarsa wuta

Spread the love

An kama wani mutum mai shekaru 30, Moturayo Olaniyi, bisa zargin kashe matarsa, Olajumoke Olaniyi, mai shekaru 25, kan rashin fahimtar juna a Legas.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Legas.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 4 ga Oktoba, 2024 da misalin ƙarfe 1 na rana.

Ya ce an samu kiran waya kan ƙoƙafin tashin hankali ga sashin ‘yan sanda na Ikorodu cewa wasu ma’auratan da suka yi aure, sun yi taho-mu-gama a cikin ɗakinsu da ke Amazing Grace Estate, Elepe, a yankin Ikorodu a jihar.

“A cikin haka, an ruwaito mijin ya daɓa wa matar wuƙa har lahira, ya kulle ta a ɗaki sannan ya banka mata wuta, yayin da ya raunata kansa.

“Bisa rahoton, tawagar jami’an tsaro sun ziyarci wurin da gobarar ta tashi, yayin da aka ga gawar matar kwance a ƙasa da rauni a ɓangaren cikinta, kuma an ceto mijin da rauni aka garzaya da shi asibiti da ke kusa, inda aka yi masa magani aka sallame shi, sannan aka kai shi hannun ’yan sanda.

“Bayan an yi masa tambayoyi da bincike na farko, an gano cewa wanda ake zargin ya daɓa wa matarsa ​​wuƙa ne a lokacin da suke fafata rikici a tsakaninsu, ya kuma yanka jikinsa da wuƙar,” inji Hundeyin.

A halin da ake ciki kuma, an ajiye gawar a ɗakin ajiye gawa na babban asibitin Ikorodu domin a duba musababbabin mutuwarta.

Sai dai ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin sanin haƙiƙanin abin da ya haddasa mutuwar matar.

By ukarofi