An haifi Alhaji Hassan Wayam a wani gari mai suna Gwadda, wanda kuma ake kira Bakin Ruba, a yankin Maradun a Jihar Zamfara, a shekarar 1956.
Mahaifinsa, Malam Muhammad babarbare ne. Mahaifiyarsa Halima Bafalasɗiniya ce. Sana’ar mahaifinsa kiɗa ce, amma wani lokacin yakan yi wa fulani waƙar kotso.
Lokacin yana ƙarami mahaifinsa ya koma wani gari mai suna Kunci da zama, gabas da birnin Gusau. Da Hassan ya ɗan girma, ya koma Mayanci, kusa da Gusau, ya zama ɗan kanikanci. To, Mayanci ya kasance bariki a lokacin, ga ƙaruwai, ’yan caca da sauran ’yan bariki. Anan sha’awarsa ta waƙa ta ƙara zurfafa musamman waƙar kukuma. Amma bai fara koyo ba sai da ya koma gida Kunci.
Nan ya fara ɗinkin kukuma da hannunsa. Duk lokacin da ya sami lokaci, ya kasance yana goge gashin kansa da hannunsa, amma a ɓoye. Da ya samu hikima sai ya sake komawa Mayanci, To sojoji sukan bi ta Mayanci, sukan yi zango a can ko ma su kwana. A haka ne ya gana da soja mai suna Ali Barau, wanda ya buƙaci matar ta ba shi Hassan, ta kai shi Zariya. Tace to ga amana.
Ali Barau ya kai Wayam Zariya a 1969, ya sauka a gidansa da ke unguwar Kanawa. Kullum da yamma sai ya kai shi barikin sojoji yana wasa da sojoji.
Hassan Wayam ya rasu a ranar Asabar, 24 ga Oktoba, 2020.
