Daga UNCLE LARABI
Da za mu iya, a ranar 1 ga Oktoba kowa kada ya fito ya zauna a gida har masu kasuwanci da ababen hawa, don nuna wa duniya da gwamnatin zalunci ta Nijeriya cewar har yanzu ba mu samu ’yancin da ya kamata a ce a na kwarorotonsa ba a duniya.
Ya yi Wuri! Kuma Ya yi kusa! Da aka ba wa Nijeriya ’yanci, ya kamata a ce a 2010 aka ba wa wannan ƙasar tamu ’yanci. Da ko ba mu TSIRA da komai ba, za mu tsira da gine-gine masu kyau na gwamnati da tituna da wutar lantarki da asibitoci da makaranta duk masu kyau na gwamnati har ma da kasuwanni masu kyau da tsari.
Haka nan ba lallai ne mu TSIRA da manyan beraye masu sace dukiyar ƙasarmu ba su ci su kaɗai su da iyalansu su bar miliyoyin mutane suna fama da fatara da yunwa da talauci suna neman abinda za su ci sau ɗaya a rana yana neman ya gagare su ko ma ya gagare su.
Tabbas da za mu daure mu jure mu aikata wannan zaman gidan ko da na rana ɗaya ne. Zai baƙanta wa gwamnati rai zai shafi tattalin arzikinta na ranar. Za ta yi asara da yawa, kuma za ta shiga taitayinta ta san cewar talakawan ƙasarfa suna cikin mawuyacin hali. Yadda gwamnatin ke neman ta gurgunta da yawa daga cikin mutanen ƙasar. Su ma sun shirya za su iya gurgunta gwamnati salim-alim! Babu makami babu fito na fito sai salon ƙaurace wa fitowa a wasu ranakun, don nuna fushi ga wannan zaluncin da ake yi wa talakawan ƙasar.
To, ba za mu iya ba. Na san ’yan Nijeriya da rashin tsari, wanda hakan shi ya jefa mu cikin wannan ƙangin bautar da shugabannin Nijeriya suke cin karensu babu babbaka suke sukuwar dawaki akan talakawan ƙasar.
Shin za mu cigaba da zama a haka ne cikin ƙangin bauta da zaluncin da shugabannin Nijeriya ke yi mana ko kuwa za mu sama wa kanmu mafita da ’yanci ranar ’yanci, wato 1 ga Oktoba???
Mu haɗu a ‘Comment Section’.
Ɗan uwanku, ƙaninku, abokinku Abdullahi Jibril Larabi (Uncle Larabi), 08065418892
