Mun dakatar da fafutikar neman tsige Ganduje daga shugabancin APC – Matasan Arewa ta Tsakiya

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU

Gamayyar ƙungiyoyin matasan Arewa ta Tsakiya ta ce ta dakatar da fafutukar da ta ke yi ta neman a tsige Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga matsayinsa na shugabancin jam’iyyar APC.

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin, Hon. Abdullahi Sale Zazzaga ne ya bayyana hakan a wata hira da DCL Hausa ta yi da shi a ranar Laraba.

Zazzaga ya ce manyansu ne su ka ja hankalinsu kan su dakatar wannan fafutuka musamman saboda taron kwamatin zartarwa na jam’iyyar da ke ƙaratowa.

Zazzaga ya ce, “Komai da ka gani ana yi ne bisa dalili. Siyaysar da mu ke, mu na yi ne don neman ƴanci. Wannan cigaban yankinmu da al’umarmu da zamana lafiyar al’umar da kuma bunƙasar tattalin arzikinsu sune a gabanmu.”

“Abinda ya faru shine, mun yi fafutuka. Kowa da ya ke faɗin ƙasar nan ya sana mun yi fafutuka. Kuma ba daina fafutuka za mu yi ba.

“Mu na wannna fafutuka ne saboda ci-gaban al’umma. Amma saidai komai da mu ke yi muna da manya. A cikin wannan tafiya da mu ke yi manayanmu sun kira mu sun zauna da mu kuma sun ce lokaci ya yi da za mu tsaya da wannnan fafutuka saboda duk Wanda ya kamata ya ji mu, ya ji mu. Wanda ya kamata ya yi magana ya yi magana. Sun umarce mu da dakatar da wannan fafutuka tun da taron kwamatin zartarwar na jam’iyyar na ƙaratowa nan da kwanaki”, inji Zazzaga.

“Sun ce mu jira mu ga me kwamatin zai yi akai duk abin da NEC ta yanke, daga nan sai mu san matakin da za mu ɗauka na gaba.”

By Babaji