Shugaban JIBWIS na Katsina ya buƙaci mahukunta su kyautata wa mabiya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatul-bidi’a Wa Iƙamatus-Sunnah (JIBWIS) na Jihar Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina, ya yi kira shugabanni a dukkan matakai su guji barnatar da dukiyar al’umma kuma su riƙa kyautata wa waɗanda su ke shugabanta.

Sheikh Yakubu Musa ya faɗi hakan ne ta wata kafar sadarwa ta ƙungiyar, inda ya ce a wannan lokaci na halin matsin rayuwa, wajibi ne shugabanni a madafun iko da ƴan majalisu da masu wadata su fito da arziƙin da Allah ya basu su tallafa wa mabuƙata.

“Ka je kasuwanninmu ko asibitoci ka ga yadda mutane suka tagayyara inda wasu magidanta suke tafiya suna barin iyalansu a saboda ba sa iya biyan kuɗin magani.”

Ya bayyana takaicinsa ga yadda shugabanni ke kashe biliyoyin kuɗaɗe wajen shirya bukukuwa baya ga al’ummarsu na kwana da yunwa.

Ya kuma yi kira ga limaman masallatan juma’a da su mayar da huɗubobinsu akan mahimmancin taimaka wa mabuƙata a musulunci.

Halin matsin rayuwa dai a Katsina ya tilasta yawaitar bara acikin al’umma yara da manya, yayin da ƴan kasuwa ke rufe shagunansu saboda rashin ciniki.

By Babaji