Sanwo Olu ya bayyana Naira 85,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan Legas

Spread the love

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta fara biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi na N85,000.

Sanwo-Olu ya bayyana wannan a daren Laraba yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV, a shirin da aka yi wa take “One on One with Babajide Sanwo-Olu.”

Yayin da aka ambaci batun mafi ƙarancin albashi, gwamnan ya ce: “Ina farin cikin sanar da ku cewa mafi ƙarancin albashi a Legas, wanda muka tattauna tare da ƙungiyarmu, ya zama N85,000 daga yau.

“Ba gasa muke yi ba, don haka ba zan ce muna biyan fiye da wasu ba; abin ya ta’allaƙa ne da irin adadin kuɗin da muke da shi da kuma ƙarfinmu,” in ji gwamnan.

Karin bayani zai biyo baya…

By ukarofi