Daga RABIU SANUSI a Kano
Dan takarar ƙaramar Hukumar Nasarawa dake Jihar Kano ƙarƙashin Jam’iyyar NNPP, Hon. Yusuf Imam da akafi sani da ‘Ogan ɓoye, ya bayyana ƙudurinsa na ganin maido da martabar ƙaramar hukumar da yake takara kan turbar da ta dace.
Ambassada Yusuf Imam ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da suke taron ƙaddamar da takara da shirin fara gudanar da yaƙin neman zaɓe a faɗin mazaɓu 11dake faɗin ƙaramar hukumar.
Ogan Boye ya tabbatar da cewa wannan takara da za su yi ba don amfanin kansu ba ne burin su yadda za su taimaki al’ummar ƙaramar hukumar su mai albarka.
”In sha Allahu ni da mataimakina Hon. Dahiru Aro dakata da Sakataren wannan tafiya Hon. Mai Kaba da sauran jagororinmu za mu yi bakin ƙoƙarinmu don mu samu yadda za mu taimaki jama’armu.
ɗan takarar ya kuma bayyana matuƙar godiyarsa wajen yadda uwar jam’iyyar NNPP ta jihar Kano ta ba su damar tsayawa takara a wannan ƙaramar hukuma.
”Kazalika muna godiya ga mai girma gwamna Abban Kanawa bisa bani dama da ya yi don zama ɗaya daga cikin manyan masu ba shi shawara a wannan gwamnati, fatan mu shi da jagoran mu Dr Rabiu Musa Kwankwaso Allah ya ci gaba da dafa masu.
”Za mu fara gudanar da zagayen kamfen neman goyon bayan jama’ar mu daga ranar Alhamis ɗin nan, inda za mu ɗauki kwanaki huɗu kafin mu kammala a mazaɓu 11 na wannan ƙananan hukumomi.
Ambassadan ya kuma buƙaci magoya bayan shi da su ƙara ba su goyon baya da addu’a don ganin sun samu nasarori a wannan zaɓe da za a gudanar.
Shi ma a nasa jawabin ɗaya daga cikin jagororin NNPP na Nasarawa Alhaji Yahuza Yankaba ya ce bayyana cewa kowane dan takara ya karbi takardar shi tare da zuwa mazabar shi dan kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen da za a gabatar.
Yahuza Yankaba ya kuma kara miƙa godiyar mu ka masoya da magoya bayan mu, bisa irin dafifin da suka yi wajen zuwa wannan taro.
Jagoran ya kuma miƙa saƙon babban jagoran NNPP na wannan ƙaramar hukuma da bai samu damar zuwa ba, bisa wasu dalilai wato Hon Mustapha Maisikeli da fatan alkhairi ga dukkan mahalarta taron.
Wakilinmu ya ruwaito cewa ƙaramar hukumar Nasarawa dai a jihar Kano na ɗaya daga cikin manyan ƙananan hukumomi 44 masu daraja da take da mazaɓu 11.
Haka kuma a lokacin taron shugabannin taron sun gabatar da wasu kwamitocin da za su lura da yadda yaƙin neman zaɓen har zuwa samun nasara cin zaɓe.
Kwamitocin sun haɗar da kwamitin bai ɗaya da Hon. ɗan Sani Hotoro wato daraktan yakin neman zaɓen zai jagoranta, sai kwamitin haɗa kan mata.
Sauran sun haɗa da kwamitin haɗin kan matasa, kwamitin tsaro, kwamitin tsare-tsare, kwamitin kuɗi sai kuma kwamitin samun nasarar cin zaɓe.
