An naɗa Thomas Tuchel a matsayin sabon kocin Ingila. Kwantiraginsa za ta fara ne daga 1 ga watan Janairun 2025.
Dan ƙasar Jamus mai shekara 51, ya zama mutum na uku da zai jagoranci Ingila wanda ba ɗan ƙasar ba, bayan Sɓen-Goran Eriksson da Fabio Capello.
Gareth Southgate ya yi murabus a watan Yuli bayan shan kashi da Ingila ta yi a hannun Sifaniya a wasan ƙarshe na Gasar Euro 2024.
Lee Carsley, wanda aka naɗa a matsayin kocin riƙon ƙwarya a watan Agusta, zai ci gaba da riƙo a wasannin Gasar Nations League da Ingila za ta yi da ƙasashen Greece da kuma Jamhuriyar Ireland a wata mai zuwa.
Tuchel, wanda ya bar Bayern Munich a ƙarshen kakar wasanni da ta gabata, ya ce: “Ina alfahari da wannan dama da aka ba ni na jagorantar tawagra Ingila.
“Na daɗe da son irin salon wasa da ake yi a ƙasar nan, kuma tuni na fara jin daɗin matsayi da na samu,” inji Tuchel.
Ya jagoranci Chelsea tsakanin Janairun 2021 zuwa Satumbar 2022 – Ya lashe Champions League da Fifa Club World Cup da UEFA Super Cup gabanin a kore shi.
