Kar ka bari alaƙar shashanci ta shiga tsakaninka da ɗalibanka matuƙar ka na son su ji tsoron ka
Daga BUSHIRA NAKURA
Yunusa Anemusu mai burin shiga aji domin bayar da ilimi ga ɗalibai, malami a Jami’ar Usman ɗanfodiyo da ke Sokoto, amma mazaunin Kano.
A tattaunawarsa da wakiliyar Blueprint manhaja, ya bayyana mana burinsa anan gaba. Ga yadda hirar ta kasance;
MANHAJA: Mai karatu zai ji daɗi idan ka faɗa mana cikakken sunanka da sunan da aka fi saninka da shi, da kuma tarihinka a taƙaice.
YUNUSA: Assalamu alaikum. Sunana Yunusa Ibrahim Adamu, ana kirana da Anemosu. An haife ni a garin Garki ta Jihar Jigawa, inda na yi karatun firamare a can. Sannan na yi karatun sakandare a Kano, na je CAS Kano na yi IJMB, sannan na yi diploma a kan English/Hausa Education. Daga nan, na fara koyarwa a makarantar Primary ta garin Kunchi a shekarar 2004. Daga nan na tafi ABU Zaria, na karanta B.A Hausa daga 2009-2012. Na yi hidimar ƙasa a Kwalejin Amir Shehu Idris da ke Zariya. Sai na fara koyarwa a Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo Sakkwato a shekarar 2018. Sai na tafi ƙarin karatu a Jami’ar Bayero, inda na yi karatun digiri na biyu a fannin Adabin Hausa, na gama a shekarar 2023. Yanzu haka Ina karatun digiri na uku (PhD) a fannin Adabin Hausa a Jami’ar Bayero da ke Kano.
Shin bayan aikin gwamnati kana wata sana’a ne?
Ina sana’ar sayar da kayan amfanin gona. Shinkafa da masara, wake da alkama da sauransu.
Ka na da aure? Idan ka na da shi, ’ya’yanka nawa?
Ina da aure mata biyu, da yara biyar.
Ko za ka iya faɗa mana irin gwagwarmayar rayuwar da ka sha?
Tabbas an sha gwagwarmayar rayuwa. Domin tun Ina shekaru 7 na rasa mahaifiyata, na tasho a ƙarƙashin kulawar matan mahaifina, wanda hakan ya haifar min da ƙalubalen rayuwa da dama. Kaɗan daga ciki shi ne, Ina sakandaren Gwamnatin Tarayya ta Daura (FGC Daura) aka cire ni, aka tura ni karatun allo a Jihar Yobe, daga nan na shiga Maiduguri sai Gombe, sai kuma na ƙarasa a Potiskum ta Jihar Yobe. Bayan na sauke Alƙur’ani mai tsarki ne, na dawo Kano, inda na ci gaba da karatun boko. A lokacin da Ina jihohin Borno da Yobe da Gombe, na yi sana’o’i iri-iri. Na yi yankan farce, na yi Shoeshainer na yi wo itace a daji na sayar, na yi wo ciyawa na sayar. Na yi wo tsamiya na sayar, na yiwo kuka na sayar, na yi tallar ruwa a tulu, na yi dako, na yi acaɓa, na yi yaron mota, da sauran ƙananan sana’o’i
ƙasashe nawa ka taɓa zuwa?
Na shiga ƙasashe da dama gaskiya. Na je Saudiyya na je Nijar da Cameroon da Chadi da Burkina Faso da Ghana da Benin Republic da Egypt da Ethiopia da Kuma Dubai.
Ko akwai ƙasar da kake son zuwa idan hali ya samu?
Ina son zuwa ƙasar Amurka da Ingila da kuma Rasha.
Me ya ja hankalinka ko me ya baka sha’awa har ka zaɓi harkar koyarwa?
Abin da ya ja hankalina na shiga aikin koyarwa shi ne sha’awar aikin. Ina so na zama mai bayar da ilimi ga waɗanda suke na ƙasa da ni. Wannan dalilin ne ya sa na samu ayyuka da yawa, amma ban mayar da hankali a kansu ba, sai aikin koyarwa.
Ya farkon fara koyarwar ka ta kasance, wacce hanya kake bi wajen shawo kan ɗaliɓanka? Kuma wacce hanya kake bi, ya ka tsinci kanka lokacin da ka shiga aji kasan cewar wasu na son yi amma suna jin tsoro ko kunya? Kai ma ka fuskanci kanka a irin wannan matsalar ko kuwa?
Farkon koyarwata kamar yadda na faɗa a makarantar firamare ne, wanda kuma aiki ne mai sauƙi kuma mai wahala. Saboda kana koyar da yara ne da ƙila ba su san komai ba, kuma kana so su sani. Wannan ya sa ake bin hanyoyin da suka dace wajen koyar da su, kamar jan su a jiki, koyarwa cikin wasa da raha da waƙe-waƙe. Wani lokacin ma har da raye-raye duk domin jawo hankalinsu su fahimci abin da ake son su koya. Da aka girma kuma, aka kai ga koyarwa a jami’a, shi kuma ya bambanta da koyarwa a Primary. Domin kana koyar da masu ilimi ne, da ake so ka ɗora su a kan wata hanya da za su zama sun dogara da kansu. Shi ma kamar na farkon dole ne malami yana buƙatar jawo yaran a jikinsa, domin koyar da su. Sannan dole ne sai malami ya zama mai fito da sabbin abubuwa da a kullum za ka nuna wa ɗaliban da suke nazarin kwas ɗin ka. Ta fuskar tsoro ko kunya kuwa, zan iya cewa gaskiya ban fuskanci hakan ba. Saboda na saba tashi a gaban mutane na yi magana, kuma a fahimce ni. Domin na yi ƙungiyoyin ɗalibai tun daga sakandare har zuwa jami’a. Wannan ya sa na samu gogewa wajen tashi na yi magana a cikin mutane. Don haka ban sami wata matsala ba.
Daga lokacin da ka fara koyarwa kawo yanzu za ka kai kamar shekara nawa ?
Daga lokacin da na fara koyarwa a Primary zuwa yanzu zan kai shekaru 17 kenan.
Ta ya kake iya haɗa harkokinka na yau da kullum da aikin ka na koyarwa ga kuma noma da sauransu?
Yadda nake haɗa aikina da harkokina shi ne, shi aikin koyarwa musamman na jami’a lokaci ne da shi, akan tsara lokutan shiga aji da kuma na yin bincike, wannan dalilin ya sa nakan yi amfani da sauran lokacin da nake da shi wajen yin harkokin kasuwancina da zuwa gona da sauransu.
Ya ka ke ganin yadda karɓuwar ka a wurin yaran da ka ke koyarwa?
Alhamdulillah! Tabbas an samu karɓuwa. Idan kin lura, ni mutumin Kano ne, kuma Ina aiki a Sakkwato. Wannan ya sa Hausar da nake amfani da ita, ta zama baƙuwa a kunnuwan ɗaliban, hakan ya sa suke tururuwar shiga duk kwas ɗin da nake koyarwa, musamman kwas ɗin aro (electiɓe) wanda duk mai sha’awa yana iya zuwa har daga wani sashen domin ya ɗauka, kuma ya koyi wani abu. Domin kwas ɗin farko da na fara ɗauka na samu ɗalibai kamar 15 ne suke yin sa, amma da na karɓa, shekara ta zagayo sai da aka samu ɗalibai kusan 50 sun yi rajista da kwas ɗin. Wannan ya nuna yadda ɗaliban suke fahimtar abin da ake koyar da su, kuma suna jin daɗin harshen.
Ta wacce hanya ka ke bi wajen ganin ka tankwara yaran wajen bin abinda ka ke so su yi?
A jami’a akwai hanyoyin da ake bi wajen ladabtar da ɗalibai ba tare da duka ko zagi ba. Irin waɗannan hanyoyi sun haɗa da, ka zamo mai sauƙi, kuma mai tsayawa a kan doka da oda. Ya zama idan ka ce e, ka tsaya a kan hakan, idan kuma ka ce a’a, shi ma ka tsaya a kan hakan. Sannan kar ka bari wata alaƙa ta shashanci ta shiga tsakaninka da ɗaliban ka, ka mayar da su kamar ƙannenka na gida. Idan ka yi haka, dole za su riƙa jin tsoron ɓata maka, sannan duk abin da ka ke son a yi, in sha Allah za a yi.
Kowa ya san koyarwa na da wahala matuƙa musamman ma ta ƙanana yara. Ko me za ka ce akan wannan?
Tabbas koyar da ƙananan yara abu ne mai wahalar gaske. Kasancewar ba su sani ba, kuma ake son ka sanar da su. Sannan ga wasa a zukatansu ga rashin sabo da mutane, ga tsoro da sauransu, tabbas akwai wahala.
Wanne irin ƙalubale ka taɓa fuskanta ga yaran ko iyayensu ko makamancin haka?
Gaskiya ni ban taɓa samun wani ƙalubale ba ko daga ɗalibai ko iyayensu. Muna girmama juna.
Waɗanne irin nasarorin ka samu game da wannan sana’a taka?
Na samu nasarorin da ba zan iya lissafa su ba a harkar koyarwa. Farko dai da aikin koyarwa ne na yi karatun digiri na ɗaya da na biyu, har zuwa na uku da nake ciki a yanzu. Wannan babbar nasara ce, wacce ba zan manta da ita ba.
Shin ka taɓa ji a ranki cewar dama ba ka zaɓi wannan layin na koyarwa ba?
Ban taɓa nadamar zama malamin makaranta ba, domin na guje wa wasu ayyukan ma saboda na zama malamin .akaranta. Kuma ba na nadama duk yadda darajar aikin yake zubewa a idanun gwamnati hakan bai sa na yi nadamar kasancewa a ciki ba.
Akwai suna da ɗalibai kan sawa malamai tun daga firamare har zuwa jami’a. Kai wane irin suna aka sa maka?
A firamare suna kirana da ‘Play’ saboda kullum muna fita wasanni da su. A sakandare kuma kamar a GGS Fatima Muhammad Gyadi-Gyadi suna kirana da ‘A Nemo su’. A jami’a kuma suna kira na da ‘Kwamared’. Sai kuma waɗanda ake faɗa a bayan ido da mutum ba zai sani ba.
Yaya ka ke kallon rayuwar da da ta yanzu?
Rayuwar da, da kuma ta yanzu akwai bambanci kamar nisan sama da ƙasa.
Wane abu ne na farin ciki wanda baza ka taɓa mantawa da shi ba?
Abin farin ciki shi ne, yadda na ziyarci ɗakin Allah da ke Makkah da kuma ziyartar kabarin Ma’aiki SAW da ke Madina.
Wane abu ne na baƙin ciki wanda baza ka taɓa mantawa da shi ba?
Abin baƙin cikin da ba zan manta da su ba, shi ne rasuwar mahaifiyata.
Meye ya ke ba ka tsoro a rayuwa?
Kwanciyar kabari ce ta fi ba ni tsoro.
Me ka fi so a yi ma kyauta da shi?
Ina so a yi min kyautar turare.
Wane abu ne ya ke saurin saka ka jin haushi?
Abin da ke saka ni saurin jin haushi bai wuce in ga mace maras kamun kai ba. Ko na ga mace mai bazar-bazar.
Wane kalar abinci da abin sha ka fi so?
Ina son tuwon shinkafa miyar busasshiyar kuɓewa da busasshen kifi.
Yanayin gari wanne ka fi so damina sanyi da zafi?
Ba na son zafi. Sanyi na fi so, domin ko da sanyi, sai na kunna fanka nake bacci.
Ko ka na da wani buri, wanda ka ke son cikawa?
Ina so na zama Farfesa, nan gaba, in sha Allah.
Meye ka ke so ga mutane?
Mutane su zama masu haƙuri. Su zama masu riƙo da addini.
Ko akwai abinda ka ke son cewa wanda ya shafe ka ko al’umma wanda ba a tambaye ka?
Abin da zan ce shi ne, mutane su zamo na gari, su yi ilimi na addini da na zamani iya ƙarfinsu. Kuma a nemi sana’a.
Su waye gwanayenka a duniya?
Gwanayena biyu ne, marigayi mahaifina da marigayi mahaifiyata.
Wacce nasiha za ka yi wa matasa musamman cima zaune waɗanda ba su son nema?
Matasan da suka zama cima-zaune, su ji tsoron Allah su nemi sana’a, saboda nan gaba su ma za su zama iyayen wasu.
Ko ka na da wanda za ka gaisar?
Ina gaishe da malamaina da ɗalibaina da yarana da sauran al’ummar Musulmai.
Fatanka ga jaridar Blueprint Manhaja?
Jaridar Blueprint Manhaja Ina muku fatan alheri.
