Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Rauda dake Rangaza da Daraktan makarantar, Imam Muhammad Yakub ya kafa da cewa tana taimakawa domin bada gudunmawa a inganta harkar lafiya a cikin al’umma.
Malam Isa Safiyanu Umar mai kula da hada-hadar kuɗi na Kwalejin kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Rauda ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a madadin darakta janar na makarantun Rauda Imam Muhammad Yakub.
Ya ce daga manufar kafa makarantar shine don taimakawa al’umma don matso da tarbiyyar yara kusa kan gina su akan samun horo akan ilimin kula da lafiya da sana’a.
Ya yi nuna cewa Daraktan kwalejin Imam Muhammad Yaɗubu ya lura da muhimmancin horar da matasa harkar kula da lafiya sai aka samar da kwalejin aka soma yin kwas a matsayin matakin sanin makama” preliminary” Ana bada horo kan abinda ya shafi harkar lafiya an soma da ɗalibi ya samu horo anan, sai ya nemi gurbi a wata makaranta ta lafiya ya cigaba ,wannan kan sa darasin ya zame masa da sauɗi.
Malam Isa Safiyanu Umar ya ce a haka sun kai matakin da ake alfahari da ɗalibai da suka sami horo a fannin lafiya a kwalejin, daga wannan mataki ne suka samu rijsta da ma’aikatar lafiya sannan suka yi haɗaka da wata makaranta a Saminaka suna bada horo akan harkar lafiya. A halin yanzu ma sun kai gaɓa ta ɗarshe suna zaman cikakkiyar kwalejin koyar da kimiyyar lafiya da fasaha nan gaba ma suna akan matakin da za a sahale musu yin ɗarin darasussuka akan lafiyar al’umma da fannin magunguna da sauran darussa.
Ya ɗara da cewa tun da fari sun soma horar da ɗalibai ne guda 15 a fannin lafiya amma cikin gajeren lokaci ɗalibai sun kai 80 har yanzu ta kai duk lokacin da suka buɗe ɗauka ɗalibai ɗaruwa suke yanzu suna da ɗalibai 115 maza da mata da malamai 15 na dindindin da kuma waɗanda bana dindindin ba.
Ya ƙara da cewa yanzu akwai darussa da suke sun kai 10 amma sun fi bawa lguda uku daga ciki muhimmanci yanzu sune” community health, medical laboratory, Public health” zuwa baɗi idan suka ɗarasa samun cikakkiyar dama za su ɗora da wasu darussan.
Malam Isa ya bayyana cewa farkon assasa kwalejin sun ci karo dai ɗalubale don al’umma da ake cikinsu da yawa basu fahimci abinda ake so ayi ba, har aka riɗa suka ana ganin kamar damfara ko cuta ake so a yi wa yara har ana bushe kunnen wasu daga ɗaliban da iyayensu amma bisa irin jajircewa da tsayawa aka gaskiya da tsari na Darakta janar na Rauda Imam Muhammad Yakub ya yi cikin ikon Allah duk an maganta wasu matsalolin musamman da aka soma samun rijista da hukumomi suke bayarwa na izini da amincewa da makarantar.
Ya ce yanzu al’umma sun fahimta sosai suna kawo ‘ya’yansu suna basu goyon baya yanzu tsakaninsu da iyayen yara sai sambarka da godiya musamman idan yaro ya yi wani abin bajinta.
Ya ce a fannin lafiya ana so mutum ya zama natsasse mai tarbiyya wajen kula da mara lafiya ta kiyaye al’ada da addininsa suna ɗoɗarin ganin ɗalibai sun ɗabbaɗa hakan duk inda suka sami kansu.
Ya ɗara da cewa Daraktan kwalejin Imam Muhammad Yaɗubu ne ɗashin baya da yake bada gudunmawa sosai a duk ɗawainiyar ta da tallafawa da shawarwari da gudunmawa da shugaban kwalejin da rijistara na kwalejin suke bayarwa.Iyayen ɗasa Dagatai,masu unguwanni suna bada goyon baya wajen ganin cigaban kwalejin dan haka yana da muhimmanci al’umma su cigaba da bada gudunmuwa don gina cigaban ilimi .
Ya ce yanzu haka kwalejin na da tsarin tallafin karatu da ake baiwa Dagatai, masu unguwanni da Dattawa ta basu dama su kawo masu hazaƙa da basira da ake basu dama su yi karatun kuma sannan akwai ɗalibai da idan suka gaza biyan kuɗin makaranta Daraktan kwalejin shi yake cika musu an kuma sahale a riɗa biyan kuɗin makarantar da kaɗan kaɗan kuɗi mai sauɗi domin a taimakawa al’umma.
Malam Isa Safiyanu Umar ya ɗara da jaddada cewa irin ƙoƙarin Daraktan janar na kwalejin Muhammad Yakub ne ɗashin bayan nasarar da ake samu domin mutum ne da yake gudanar da abubuwa ba don mai zai dawo ba na riba ko wani abu tunda aka fara makarantar ma babu wata rana da za a ce ya amfana da kuɗin makaranta sai nasa ma da yake sawa a ciki don gudanar da ita.
Shi ma ɗaya daga malamai a kwalejin Malam Nura Aliyu ya ce duk abinda ake buƙata wajen koyar da ɗalibai an samar da shi ya sa ma suka zo suna bada gudunmawa ta koyarwa domin akwai kayan koyarwa da koyo na zamani na abinda ake buɗata. In aka lura jihar Kano ita ce mafi yawan al’umma, samar da irin waɗannan makarantu na lafiya za su taimakawa makarantu na gwamnati samun gurabe na yara da za su yi karatu.
Malam Nura Aliyu yace akwai buɗatar ma’aikatan lafiya su wadata lungu da saɗo domin a wannan kwalejin ana koyar da waɗanda za su kula da lafiya ne a matakin farko da ake da ɗarancin su, samar da irin waɗannan makarantu da baiwa ɗalibai kyakkyawar horo zai inganta harka kula da lafiya da magance cututtuka daga matakin farko zai taimakawa gwamnati da al’umma wajen daƙile yadɗuwar cututtuka.
A nasa ɓangaren rajistara na Kwalejin kimiyyar lafiya da fasaha na Rauda, Abubakar Salihu ya bayyana cewa suna yin tsare-tsaren ɗaukar yara da suka cancanta domin sai wanda yake da karatu na darussa a ɓangaren kimiyya da lissafi ya cika ɗa’ida shi ake baiwa dama ya yi karatu.
Ya ce ba su da wata matsala da Gwamnati sun zo sun ga makarantar sannan suka sahale damar gudanar da ita haka sauran hukumomi na fannin lafiya na ɗasa sun gamsu da yadda ake tafi da ita bisa sahalewa ta doka.
Rijistaran na kwalejin kimiyyar lafiyar da fasaha ta Rauda ya ce yanzu akwai ƙarancin ma’aikatan lafiya zaka je asibiti kaga mutum biyu uku sune ke aiki musamman a ɗauyuka da karkara sai kaga basa iya aiki awa 24 saboda ƙarancin ma’aikatan ya kamata a ce kowace mazaɓa tana da asibiti ɗaya da zai riɗa kula da lafiya kowane lokaci, amma saboda ƙarancin ma’aikatan lafiya hakan ba zai yiwu ba don haka muna da buƙatar makarantun lafiya masu zaman kansu da yawa da zasu bada horo ga matasa wajen kula da lafiya.
Malam Abubakar Salisu ya yi kira ga Gwamnati ta tabbatar da makarantu na lafiya suna bin tsarin dokoki yanda za a riɗa bada ilmi ingantacce mai nagarta domin ya amfani al’umma domin in akayi sakaci abin ya tafi sakaka ba zai haifar da ɗa mai ido ba, don haka gwamnati ta sa ido wajen ganin makarantun lafiya suna da tsari mai inganci.
