Ganduje zai cigaba da zama shugaban APC sakamakon yiwuwar ɗage babban zaman Majalisar Zartarwar jam’iyyar zuwa 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Alamu sun nuna cewa shugabancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC ka iya dakatar da taron ƙaddamarwa na babban kwamitin Zartarwa na Ƙasa, NEC zuwa 2025.

An samu wasu bayanai daga Sakatariyar APC kan cewa ayyuka da suka yi wa Shugaba Tinubu yawa da rashin kasancewar sa a ƙasa su ne dalilan da suka sa za a ɗage zaman.

Wata majiya ta ce, saboda Shugaba Tinubu ba ya ƙasa ya sa aka dage zaman a karon farko wanda aka tsara yin sa tun a watan Satumban da ya gabata.

Duk da cewa ba a samu ƙwaƙƙwaran dalilin da ya sa aka dakatar zaman ba, Sakataren Labarai na Ƙasa, Felix Morka ya ce za a sanar da wata rana daga baya wadda kawo yanzu ba a bayyana ta ba.

Haka ma wata majiya daga Fadar shugaban ƙasa ta ce, Shugaba Tinubu da manyan ƴaƴan jam’iyyar su na jin-daɗin shugabancin Ganduje tare da amincewa da salonsa na gudanar da jami’yyar.

Kawo yanzu dai ana sa ran saka sabuwar rana da za a yi zaman bayan dawowar shugaban ƙasa daga tafiyar da ya yi.

By Babaji