Daga USMAN KAROFI
Hukumar samar da wutar lantarki ta ƙasa ta bayyana cewa an sake samun saukar rumbun lantarki na ƙasa wanda ya jefa ƙasar cikin duhu baki ɗaya wajen ƙarfe tara na safiyar Asabar.
Wannan dai shine karo na uku da rumbun ke sauka cikin mako guda. Wanda hakan na nufin runbun lantarkin ya sauka sau takwas a cikin wannan shekarar.
Duk da wannan irin gazawa, hukumar TCN ta bakin kakakin ta Ndidi Mbah ya bayyana an samu cigaba sosai da kusan kashi 70 duba da yanayin yadda abubuwa suke shekaru biyu baya.
Sai dai ministan Lantarki ya bayyana cewa, wannan matsalolin suna faruwa ne saboda tsufa da wuraren nan su kayi da kuma shekara da shekaru da aka ɗauka ba wani gyaran kirki.
Ministan ya cigaba da cewa, dole ne mayar da hankali wajen samar da wutan shine zai rage yawan faruwar haka, duba da yanzu Nijeriya ta dogara da layin samar da wuta guda ɗaya ne kacal, shiyasa da ya samu mastala jihohi 36 suke fama.
