
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Jihar Kogi ta ce babu dokar taƙaice zirga-zirgar matafiya a yayin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi a ranar Asabar.
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Jihar (KOSIEC), Mista Mamman Nnda-Eri ya bayyana hakan wa ‘News Agency Nigeria’ a Lokoja, babban birnin jihar a ranar Juma’a.
Nnda-Eri ya tabbatar wa matafiya samun gudanar da harkokinsu cikin sauƙi ba tare da musgunawa ba kamar yadda Kwamishinan Labarai, Mista Kingsley Fanwo ya faɗa a cikin wata sanarwa, da ya ke magana kan taƙaice zirga-zirgar ababen hawa daga ƙarfe 7 na safe zuwa 4 na yamman ranar Asabar.
Fanwo ya ce, an yi hakan ne don tabbatar da gudanar da zaɓukan cikin lumana a ƙananan hukumomi 21 na jihar.
Shugaban KOSIEC ya ce dokar ta taƙaitu ne ga mazauna jihar kaɗai, ban da matafiya da ke wucewa ta titunan jihar.
Tuni dai gwamnatin jihar ta umarci jami’an tsaro su tabbatar da an kiyaye doka da oda don kammala zaɓen cikin lumana kamar yadda aka tsara shi.
