
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya jinjina wa tsohon shugaban mulkin soji, Janar Yakubu Gowon kan cika shekaru 90 a duniya, ya na mai cewa hakan abu ne wanda ya kamata a ce ƙasa ta yi murna a kai.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a Abuja a lokacin lakcar bikin zagayowar ranar haihuwar Gowon a jiya Juma’a inda ya yi godiya ga Ubangiji ganin yadda Ya sa Gowon ya kai shakaru 80 a duniya.
Shugaban taron, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III ya jinjina wa tsohon shugaban ƙasar inda ya ce shi ɗin jigo ne na haɗin kai da mutuntawa a Nijeriya.
Ya ce, Nijeriya ta yi sa’ar samun shugaba irin Gowon wanda ya yi tsawon rai da kuma lafiya inda a saboda juriyarsa ne, ya tabbatar da zaman lafiya da haɗin-kai a tsakanin al’umma.
A shekarar 1966 ne Gowon ya zama shugaban ƙasa a Nijeriya bayan wani juyin mulki da ya gudana inda ya shafe shekaru sama da takwas a karagar mulki.
