
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Hisbah a Jihar Kano, ta tabbatar da kama Kwamishinan Ayyuka na Musamman na Jihar Jigawa, Auwal Ɗanladi Sankara bayan gano shi da aka yi a wani kango tare da wata matar aure.
An kama shi ne bayan wani bincike da ake yi kan wasu ƙararraki da aka shigar game da zargin sa da ƙula haramtacciyar alaƙa da matar.
Darakta-Janar na hukumar, Dakta Abba Sufi, ya ce an kama kwamishinan ne bayan gudanar da wani bincike na sirri sakamakon ƙara da mijin matar, Nasiru Bulama ya shigar kan zargin mutumin da yin lalata da matarsa mai suna Tasleem Baba Nabegu wacce mahaifiya ce ga yara biyu.
Daraktan ya ce, lallai sun kama kwamishinan tare da matar a wani kango wanda mallakinsa ne sakamakon bibiyar sa da suka yi ta yi.
Baya ga hukumar ta Hisbah, an kuma shigar da ƙarar lamarin ga ƴan sandan Kano da takwarorinsu na DSS.
Bugu da ƙari, Dakta Sufi ya bayyana cewa, ana gudanar da bincike akan kwamishinan game da wasu cibiyoyin harakokin miyagun ƙwayoyi da karuwanci da aka yi basajan su a matsayin otal-otal wanɗanda aka sanya wa sunaye ‘Picklock’ da ‘360’.
A ranar Litinin ne za a gurfanar da kwamishinan a gaban kotu kan tuhumar sa game da haramtacciyar alaƙar da kuma harkar miyagun ƙwayoyi.
