Nijeriya ta ƙarfafa alaƙarta ta kasuwanci da ƙasar Sweden

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne Nijeriya ta ƙula yarjejeniyar cimma matsaya ta MoU tsakanin ta da kamfanin telekom, Ericsson kan samar da sabis mai ƙarfin 5G.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar ƴan Nijeriya inda aka ƙula yarjejeniyar wadda an yi ta ne don a sanya Nijeriya ta zama ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi amfani da 5G wajen harkokin ingantayya na fasahar zamani.

An gabatar da taron ne a yankin Arewacin Stockholm da ke Sweden wanda ya zama fage na ƙarfafa alaƙa tsakanin ƙasashen biyu.

Ciki wata takarda da mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nwocha ya fitar, ya ce ƙarfin sabis ɗin 5G ya ninka 4G sau 100 a sauri wanda zai ƙara sauƙaƙe wa al’umma gudanar da harkokin kasuwancinsu cikin takaitaccen lokaci da kuma inganci.

Ministan Sadarwa, Dakta Bosun Tijani wanda shi ya rattaɓa hannu a madadin gwamnatin Nijeriya, ya ce MoU da aka yi za ta taimaka wajen samar da ci-gaba cikin ƙanƙanin lokaci da bunƙasa harkar tattali arziƙin Nijeriya.

Ministan ya kuma ce su na amfani da damar ziyarar da Shettima ya kai wajen ƙarfafa alaƙa tsakanin Nijeriya da kamfanonin sadarwa don samar da ci-gaba mai ɗorewa a Nijeriya.

Haka nan, Mataimakin shugaban ƙasar ya gana da Firaministan ƙasar, Ulf Kristersson inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka alƙanta ƙasashen biyu musamman kan faɗaɗa harkokin kasuwanci, haɗa hannu kan lamuran tsaro da makamantansu.

By Babaji