Ɓarayi sun jefa Kano da Kaduna a duhu sakamakon lalata kayan wuta

Spread the love

Ɓarayi sun lalata tagwayen ginshiƙai guda biyu a kan mahimman layukan wutar lantarki na 330kV Shiroro–Kaduna na 1 da 2, wanda ya jefa wasu yankunan Kano da Kaduna cikin duhu.

Kamfanin rarraba eutar lantarki na Nijeriya (TCN) ya bayyana a ranar Juma’a cewa ginshiƙan, T133 da T136, sun samu gagarumin lalacewa, wanda ya haifar da katsewar wutar lantarki ga wasu sassan Arewa maso Yamma, ciki har da Kaduna da Kano.

An gano wannan lamarin ne lokacin da ɗaya daga cikin layukan wutar ya samu matsala, sannan ba da daɗewa ba na biyun ya samu matsala, wanda ya sa TCN ta haɗa kai da ƙungiyoyin tsaro na gida don ƙara tsaurara tsaro a yankin da abin ya shafa. Ofishin yankin Shiroro na TCN ya bayyana cewa an sami matsala mai tsanani a layukan a wurare da dama.

“Bincike ya nuna cewa wannan ba lalacewar na da nasaba da aikin ɓata gari,” in ji mai magana da yawun TCN Ndidi Mbah. “Muna aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro don tabbatar da tsaron yankin, wanda aka gano cewa yana fuskantar barazanar ‘yan bindiga, abin da ke kawo haɗari ga kayan aikinmu da ma’aikatamu.” A cikin wani yunƙurin gaggawa ga wannan matsalar, TCN ta aika da sabbin kayan aikin gyare-gyare zuwa wurin domin daidaita lamarin.

Akwai shirin sake gina ginshiƙan da aka lalata domin dawo da layukan wutar da suka lalace.

“Injiniyoyin mu sun hanzarta samar da wata hanyar wucin gadi don tabbatar da ci gaba da rarraba wutar lantarki,” in ji Mbah. “Yanzu haka muna amfani da layin 330kV Kaduna–Jos don isar da wutar lantarki ga yankunan Kaduna da Kano a matsayin wani mataki na wucin gadi.

By ukarofi